Layukan MTN suna taimaka wa Boko Haram – Buhari

Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan rashin rufe layukan waya marasa rijista wadanda  kamfanin MTN bai yi ba, inda ya ce hakan ya taimakawa kungiyar Boko Haram. Yana magana ne a karon farko a bainar jama’a tun bayan da aka ci kamfanin tarar Dala biliyan 5 da miliyan biyu sakamakon rashin karasa rijistar […]

Layukan MTN suna taimaka wa Boko Haram – Buhari

Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan rashin rufe layukan waya marasa rijista wadanda  kamfanin MTN bai yi ba, inda ya ce hakan ya taimakawa kungiyar Boko Haram.

Yana magana ne a karon farko a bainar jama’a tun bayan da aka ci kamfanin tarar Dala biliyan 5 da miliyan biyu sakamakon rashin karasa rijistar layukan wayar abokan cinikin kamfanin.

Shugaban ya yi wannan magana ne lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, a fadarsa da ke Abuja.