Layyar Bana: Tsada a cikin kogin talauci
Ragunan da aka sayar kan Naira dubu 200 a bara yanzu farashinsu ya tashi zuwa Naira dubu 500.
Yayin da gobe Lahadi in Allah Ya kai mu za a yi Babbar Sallar bana, rahotannin da wakilanmu suka tattaro mana sun nuna cewa bikin Sallar na bana zai gudana ne a cikin kogin talauci a daidai kuma lokacin da ake fama da tsadar rayuwa da kunci.
A Abuja, Aminiya ta gano cewa magidanta da dama da suka saba sayan raguna don yankawa a Sallar Layya suna cikin halin zulumi sakamakon gaza yin hakan saboda tsadar rayuwa da al’ummar kasar nan ke fuskanta.
Yawancin wadanda Aminiya ta zanta da su a yankin Birnin Tarayya Abuja, sun yi korafin cewa tsadar kayan abinci ba za ta ba su sukunin sayen dabbar Layya ba, wadda ita ma farashinta ya karu da ninki biyu zuwa uku.
Wani matsakaicin ma’aikaci a Abuja mai suna Sani Ahmad, ya ce zuwa ranar Talatar da ta gabata saura kwana 5 a yi Sallar ba ya da abin da zai sayi dabbar Layya sakamakon yadda abincin yau da kullum ke cinye da kudin albashinsa.
Ya ce akwai ma’akata da dama da ke sama da shi da suke da korafi irin nasa.
Abubakar Ibrahim, wani dan kasuwa a Abuja ya ce zai yi wuya ya iya sayen dabbar Layya a bana saboda farashinsu da ya daga sosai, ga kuma nauyin kasuwa da yake fama da shi.
Ya ce ya gwammace karkata da kudi ta bangaren noma da yake yi a bana sakamakon tsadar kayan abinci.
Aminiya ta ziyarci Babbar Kasuwar Dabbobi ta Abuja da ke Dei-Dei inda yawancin masu sayar da dabbobi a kasuwar, suka yi korafin rashin ciniki.
Sun ce lamarin na zuwa ne a lokacin da adadin dabbobi da aka saba kaiwa kasuwar ya ja baya saboda raguwarsu a wasu jihohin Arewa da ke gaba-gaba a wajen kiwonsu kamar Zamfara da Katsina da Sakkwato da matsalar tsaro ta haifar.
Alhaji Uzairu Dan-Kundalo daga Jihar Jigawa ya ce haka kuma wasu masu kiwon dabbobi ko sayar da su da ke kawo ragunansu zuwa Abuja a lokacin Sallar, da alama a bana sun gwammace sayar da dabbobin a jihohinsu saboda tsadar kudin mota da shigowar damina, da suke jin ba za su bar gonakinsu ba.
Ya ce a baya ma’aikatu da kamfanoni da ke Birnin Tarayya kan sayi dabbobi da yawa daga hannunsu don rarraba su ga ma’aikatansu.
“Sai dai a yanzu wadanda ke saya daga wannan bangaren kadan ne kawai, haka ma dadaikun mutane da ke sayen biyu zuwa 10 don raba su ga makusantansu sun ja baya a dalilin tsadar rayuwa,” inji Dan-Kundalo.
Binciken Aminiya ya gano cewa, Kasuwar Dabbobi ta Dei-Dei ta rabu biyu inda ake da bangaren ’yan kasuwan dindindin da ke sayar da dabbobinsu a cikin rumfuna da kuma tsakiyar kasuwa.
Akwai kuma bangaren baki da suke zuwa a lokacin hadahadar Sallah kadai, da aka ware masu wuri a gefen kasuwar, da ba ko wane mai shigowa ba ne zai iya gano su.
Alhaji Haruna Ahmad da ya kai raguna kasuwar daga garin Gangalawai a Karamar Hukumar Darazo a Jihar Bauchi, ya ce tsadar abincin dabbobi da ya ninka daga bara zuwa bana, na cikin abubuwan da suka kara tsadar dabbobi a bana.
Ya yi misali da dusa da a bara ya ce sun saye ta a kan Naira dubu 12 zuwa dubu 13. Ya ce sai ga ta ta kai Naira dubu 23 zuwa dubu 24 a bana.
Dan kasuwar ya ce haka lamarin yake a farashin kowar wake da suka saya Naira 6,000 a bara, amma a bana ta kai Naira 12,000 a yayin da farashin kaikayin dawa da a bara aka sayar kan Naira 3,000 a bara, a bana ya kai Naira 7,000.
Ya ce a bangarensu na baki da ake dauka a matsayin masu rangwame, ana iya samun karamin rago da ya kai yin Layya a kan Naira dubu 100, sabanin Naira dubu 60 da aka sayar a bara.
Ya ce matsakaicin rago na kaiwa Naira dubu 250 zuwa dubu 300, sabanin bara da ake iya samu a kan Naira dubu 150.
Dan kasuwar ya ce babban rago da aka turke na kamar shekara 3, na kaiwa Naira dubu 700 zuwa dubu 800.
Ya ce akwai koma-baya wajen ciniki a bana idan aka kwatanta da bara a kwatankwacin ranar zantawar, wato kwana biyar kafin Sallah.
Sai dai ya ce suna fatar samun ciniki a lokacin da zai rage kamar kwana uku kafin Sallah har zuwa ranar Sallah, lokacin da ya ce yawancin ma’aikata suka fi sayen dabba saboda karancin wuraren ajiye su a gida.
Daga Bauchi
Sai dai duk da tsadar dabbobin akwai dabbobin da yawa a kasuwannin dabbobi da ke Jihar Bauchi, kuma har wasu kananan kasuwanni masu sayar da dabbobin suka bubbude a unguwanni don saukaka ya wa masu sayen dabbobin layyar.
Da yawa daga cikin masu sayar da dabbobi da Aminiya ta zanta da su a Kasuwar Shanu da ke Bauchi sun ce farashin ya karu ne sakamakon matsalolin cire tallafin man fetur da faduwar darajar Naira da rashin tsaro a jihohin da sai an bi ta cikinsu a je kasashen makwabta da ake sayo dabbobin.
Sarkin Tuken Bauchi Alhaji Musa Firo ya ce “Babu abin da ya tsawwala farashin dabbobi kamar cire tallafin mai, amma mu nan Bauchi muna zaune lafiya.
“Za ka iya zuwa da kudinka a buhu ka shiga kasuwa ka sayi dabbarka ka fito ba abin da zai same ka, kuma saboda zama lafiya har masu sayar da dabbobi daga jihohin Katsina da Zamfara da Filato sun dawo Bauchi suna kasuwanci.
“Amma cire tallafin mai shi ya haifar da tsadar dabbobin.”
Wani mai sayar da dabbobi Alhaji Ali Mai Rago ya ce a shekarun baya sukan je Fallomi har Nijar su sayo dabbobin a irin wannan lokaci amma bana tsadar kudin mota da rashin tsaro a jihohin Katsina da Sakkwato da Zamfara ko Borno ta inda za a bi a shiga kasashen Kamaru, Nijar da Chadi sun sa lamarin ya yi tsada.
A dukkan kasuwannin da wakilinmu ya zagaya farashin rago ya kama daga Naira dubu 50 ne da dubu 100 da dubu 150 da dubu 200, har zuwa Naira miliyan daya gwargwadon kyau da girmansa.
Akasarin masu sayen dabbobin, sun ce idan mutum ya je Kasuwar Mararrabar Liman Katagum a Karamar Hukumar Bauchi ko Nabordo a Karamar Hukumar Toro ko Gadar Maiwa a Karamar Hukumar Ningi ragunan sun dan fi sauki.
Malam Ahmad Tijjani Kolo da ke harkar saye da sayar da shanu da raguna ya ce lamarin yanzu sai a hankali saboda saniya mai kyau ba ta kasa da Naira dubu 250.
Kuma akan samu san Naira miliyan daya zuwa miliyan uku. Aminiya ta lura cewa duk da dabbobin sun yi tsada, amma akwai su da yawa a kasuwannin.
Wani mai sayar da dabbobi Alhaji Abdulbaki Yakubu Sarkin Bar, ya ce zuwa Lahadin da Aminiya ta tuntube shi babu masu sayen dabbobi, amma in sun samu kudi suna sara.
“Ka ga yau na je Kasuwar Durum na sayi raguna biyar saboda sa rai da tsammanin idan aka yi albashi mutane za su saya kuma muna sa ran kafin Sallah Gwamnatin Jihar Bauchi da Alhaji Bala Wunti da manyan ’yan siyasa musamman ’yan majalisa za su saya su raba wa jama’a.
“Wannan tsammani ne zai hana mu faduwa kamar yadda yake faruwa kowace shekara.”
Wakilinmu ya ci karo da mutane da dama da suke zuwa suna taya ragunan layyar da niyyar in Allah Ya yiamusu budi su saya, amma farashin ya musu tsada shi ya sa suke tayawa don kimtsi kafin a samu albashi ko tallafi daga masu hannu da shuni.
Ibadan
Farashin raguna ya tashi fiye da kima a Ibadan da sauran garuruwan Jihar Oyo.
A ziyarar da Aminiya ta kai manyan kasuwannin dabbobi na Akinyele da Alesinloye a Ibadan ranar Litinin ta gane wa idanunta yadda kasuwannin suka cika da manya da kananan raguna da awaki ba tare da yawan jama’a da suka saba rububin sayen ragunan Layya a irin wannan lokaci a baya ba.
A Kasuwar Dabbobi ta Akinyele karamin ragon da aka sayar kan Naira dubu 70 a bara farashinsa ya ninka zuwa Naira dubu 150.
Sai manyan raguna da aka sayar a kan Naira dubu 200 a bara yanzu farashinsu ya tashi sama zuwa Naira dubu 500.
Alhaji Abdulganiyu Dankasa dillalin raguna a Kasuwar Akinyele ya ce “Mutane sun ba sa zuwa sayen raguna ne saboda karancin kudi.
Wasu kuma saboda tsadar dabbobin in suka bari zuwa wannan lokaci ya sa suka sayi ragunansu tun lokacin Karamar Sallah.
A bangaren wadanda suka saba sayen raguna 20 zuwa 50 domin raba wa jama’a, ya ce yanzu sun rage zuwa 10 ko 20.”
Wani mai suna Tanko Isa ya ce “Na sayo raguna 50 daga Katsina zuwa nan Ibadan amma na yi bakin cikin ganin yadda ake samun karancin masu saya.”
Shi kuma Dalha Abdu cewa yayi “Daga cikin raguna 15 da na kawo su akwai bakwai da aka ba ni amanar sayarwa.
“Takaicina shi ne ban san bayanin da zan yi ga mutanen da suka ba ni amanar ba musamman idan farashin ragunan ya karye kafin ranar Babbar Sallah.”
Binciken Aminiya a Kasuwar Alesinloye ya gano yadda mutane suka kawo raguna daga sassan Arewa zuwa Ibadan inda suke kukan karancin masaya.
Binciken ya kuma gano akwai wasu ’yan kasuwa masu sarin dabbobi daga manyan kasuwanni zuwa kanana wadanda aka samu raguwarsu a bana.
“Na yi kasadar saro matsakaitan raguna a kan Naira dubu 150 zuwa dubu 200, amma yau kwana biyu ban sayar da ko daya ba.
“A bara a daidai irin wannan lokaci mun yi cinikin fiye da raguna 50,” in ji wani dan sari mai suna Azeez Komolafe.
Wasu Hausawa da aka zanta da su sun ce shekara 20 da suka saba sayen ragon Layya a kowace shekara ba su taba fasawa ba.
“Amma a bana akwai alamar ba za su iya ba, a dalilin karancin kudi.
“Tunda wannan lamari ya rikice ina ganin zan nemi ’yan uwa Musulmi mu hada kudi mu sayi bajimi kamar yadda addinin Musulunci ya amince,” in ji daya daga cikinsu.
Wani kuma ya ce, “Rago uku na saya a bara na yi Layya da su, amma a bana babu kudin sayen ko daya.”
Binciken ya nuna cewa marasa karfi da suka saba samun ragunan Layya kyauta daga hannun masu hali da ’yan siyasa sun yi zaman dirshan a gidajen mutanen suna jiran tsamani.
A baya attajirai da ’yan siyasa kan yi rabon raguna ga jama’a kwana 10 kafin ranar Sallah, amma a bana lamarin ya canza.
A daidai wannan lokaci ne kuma jami’an tsaro suka yi nasarar kama barayin Raguna da yanzu haka suke gudanar da bincike a kansu.
Kaduna
Haruna Allah Ya Amfana mai sayar da rago a Zangon Kaduna ya bayyana cewa duk da yanayin tattalin arziki jama’a na ci gaba da zuwa sayan ragunan Layya.
Sai dai a cewarsa, ragunan sun dan yi tsada, amma daidai kudin mutum daidai abin da zai iya saye domin yin Layya.
Ya bayyana farashin ragunan da cewa masu ’yan daidai su ne ake sayarwa a kan Naira dubu 75, zuwa dubu 80.
“Muna kuma da ’yan manya da kudinsu ya fara daga Naira dubu 100 zuwa 120, zuwa manyan da ake sayarwa Naira dubu 600.
“Ko a ’yan kwanakin nan na sayar da manyan ragunan daga Naira dubu 120 zuwa sama,” in ji shi.
Ya kara da cewa taimakon Allah ne amma fa kasuwar babu matsala tunda dai jama’a na ci gaba da zuwa saye duk da tashin farashin idan aka yi la’akari da bara yadda ake sayar da ragunan.
Malam Musa Danlami mai sayar da raguna a kan Titin Waff da ke Kaduna, ya ce tsadar rayuwa ta shafi kowane fanni a kasar nan.
Ya ce kudin ciyar da dabobbin ya tashi matuka kuma hakan na da alaka ne da janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi.
“Kada ku ga laifinmu dangane da tashin farashin raguna, saboda dole ne mu ciyar da su da kuma iyalanmu,” in ji shi.
Sani Musa da ke sayar da raguna a Kasuwar Barnawa ya ce har yanzu farashin bai fi karfin matsakaitan Musulmi da ke da halin yin Layya ba, sai dai ya kara da cewa rashin tsaro ma ya taimaka wajen tashin farashin dabbobi a bana.
Fasto Yohana Buru ya yi kira ga masu sayar da raguna su taimaka wajen rage farashin dabobbin domin bai wa Musulmi damar yin Layya ga wanda yake da hali.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci wasu kasuwannnin dabbobi a jihar domin ganawa da masu sayar da dabbobin.