Lead British: An rufe makaranta kan cin zalin daliba a Abuja
An rufe makarantar Lead British International da ke Abuja bayan rikicin cin zalin da wasu daliban makarantar suka yi ga dayarsu.
An rufe makarantar Lead British International da ke Abuja bayan rikicin da da ya biyo bayan yaduwar bidiyon wasu daliban makarantar sakandaren da suka ci zalin dayarsu.
Hukumar gudanarwar makarantar mai zaman kanta ta sanar da rufe ta na tsawon kwana uku sakamakon dambarwar.
A cikin wani bidiyo da ya karade kafofin sada zumunta an ga wasu daliban makarantar mata su biyu suna cin zalin wata daliba, inda suke da gaura mata mari.
A gefensu kuma wani dalibi namiji yana dariya, a yayin da wasu daliban suke zuwa masu marin nata, ita kuma babu abin da ta yi.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce da tare da jawo Allah-wadai gami da kiraye-kirayen neman hukumar makarantar ta dauki mataki.
A ranar Talata gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rufe makarantar, a cewar wani jami’in makarantar a cikin wani bidiyo.
Jami”in ya ce an rufe makarantar ce bisa umarnin Ma’aikatar Mata, saboda haka “Daga yau an rufe makarantar Lead British International, Abuja, har tsawon kwana uku.
Mai magana da yawun yan sadan Abuja, SP Josephin Adeh, ta ce runduanrsu ta tura jami’anta makaran domin yin bincike kan lamarin.
Tun da farko hukumar makarantar ta fitar da sanarwa tana mai la’antar cin zarafin da aka yi wa dalibar.
Sanarwar ta kara da cewa hukumar makarantar na tattaunawa da bangaren wadda aka ci zalin da wadanda suka doke tan, domin ganin an yi mata adalci da kuma daukar matakin da ya dace.
Ta kara da cewa ta kafa kwamitin bincike kan bidiyon da kuma na ladabtarwa kan lamarin, gami da kokarin ba da shawarwari da kulawa ga wadda aka ci zalin.