Legas na asarar tiriliyan 4 duk shekara sakamakon cunkoson ababen hawa
Binciken ya ce za a iya amfani da kuɗaɗen wajen ayyukan yara ƙasa
Wani sabon bincike ya gano cewa Jihar Legas, wacce ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya na tafka asarar Naira tiriliyan hudu duk shekara saboda cunkoson ababen hawa.
Binciken, wanda Cibiyar Bincike ta Danne ta fitar mai taken “Musabbabin Cunkoson Ababen Hawa a Legas”, Bankin Masana’antu da kuma Cibiyar Kudi ta Afirka, ya kuma jaddada muhimmancin gaggauta yin aiki domin shawo kan matsalar.
- Jami’an tsaro sun hana ’yan NNPP yin sallar neman nasara a Kano
- Boko Haram Ta Ba Mazauna Yankunan Borno 8 Kwanaki 3 Su Tashi
An gabatar da rahoton je ranar Laraba a Legas.
A cewar Shugaban cibiyar ta Danne, Franca Ovadje, za a iya sauya akalar kudaden da ke zirarewa zuwa muhimman ɓangarori irin su ilimi da lafiya da ayyukan raya kasa.
Binciken ya kuma ce yawan al’ummar Jihar da ya kai miliyan 21 ba a amfani da shi yadda ya kamata sakamakon tsaikon da cunkoson yake kawo wa jihar wanda hakan yake shafar ci gaban tattalin arzikinta.
Rahoton ya ce ko da yawan jama’ar ya ninka hakan, kamata ya yi a ce ci gaban da ake samu ya ninka hakan.