Legas za ta yi wa mazauna 10m rajista a wata 5
Gwamnatin Jihar Legas ta ce za ta yi wa mazauna jihar miliyan 10 da rajistar katin shaidar zama, domin tarawa a rumbin adana bayanan jihar daga yanzu zuwa karshen shekarar 2022. Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan ranar Laraba a bikin sake kaddamar da fara aikin bada katin shaidar zama dan jihar da […]
Gwamnatin Jihar Legas ta ce za ta yi wa mazauna jihar miliyan 10 da rajistar katin shaidar zama, domin tarawa a rumbin adana bayanan jihar daga yanzu zuwa karshen shekarar 2022.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan ranar Laraba a bikin sake kaddamar da fara aikin bada katin shaidar zama dan jihar da ta fara, wanda ya ce shi ne irinsa na farko a Yammacin Afirka gaba daya.
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan sabon karin kudin fetur
- Ambaliya: Majalisa ta bukaci Gwamnati ta kai wa al’ummar Bauchi dauki
Gwamnan ya kuma ce Hukumar yiwa mazaunan Rajista ta Jihar wato LASRRA, yanzu haka ta yiwa mutane miliyan shida da rabi rajistar, kuma tana fatan kara yiwa wasu miliyan goman kafin karewar shekarar 2022.
Hukumar LASRRA din dai an kirkire ta ne tun a zamanin gwamnatin tsohon Gwamnan jihar Babatunde Raji Fashola, da zummar zamowa ma`adanar tara bayanana al`ummar jihar, domin tsara jihar da kasafi daidai da bayanan da ta tattara.
Sake kaddamar da tsarin da Gwamna Sanwo yayi a yanzu ya ce ya yi shi ne domin rungumar chanji mai amfani ne, da kuma yin kafada da kafada da kasashen da suka cigaba da Gwamnatinsa ke yi.
Haka zalika ya ce Bankin Sterling yanzu haka ya zuba jarin Naira Biliyan uku a aikin, in da Gwamnan ya kwatanta shi a matsayin budaddiyar sheda mai kyau da ke nuna alherin da ka iya tasowa idan aka samu Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu sun hada kai don ciyar da kasa baki daya.