Leicester City ta raba gari da Brendan Rodgers

Rodgers ya jagoranci Liverpool da Celtic kafin ya koma Leicester City a Fabrairun 2019.

Leicester City ta raba gari da Brendan Rodgers

Brendan Rodgers

Leicester City ta sallami kocinta Brendan Rodgers bayan kulob din ya sha kashi a hannun Crystal Palace a ranar Asabar.

Wannan ne karo na biyar da ake lallasa kungiyar a wasanni shida da ta buga a Gasar Firimiya Ingila.

A wani sako da kulob din ya wallafa a shafinsa na intanet, ya bayyana cewa “Kungiyar Leicester City ta cimma matsaya da Brendan Rodgers, inda zai bar kulob din bayan ya shafe shekara hudu a matsayinsa na kocin kulob din.

“Brendan zai bar filin wasa na King Power a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi samun nasara a tarihin kulob din, bayan ya kai mu ga nasarar daukar kofin da muka dade muna son dauka na FA Cup a 2021,” in ji Leicester City.

Haka kuma kulob din ya kara da cewa a cikin matakai mafi girma a gasar Firimiya da kulob din ya kai, Brendan ne ya kai kungiyar matakin har sau biyu da kuma zagayen kusa da na karshe da kulob din ya kai a karon farko a gasar zakarun Turai ta Europa League a 2022.

Rodgers dai ya jagoranci Liverpool da Celtic kafin ya koma Leicester City a Fabrairun 2019.

Shi ma mataimakin kocin Leicester City Chris Davies da kuma kocin da ke kula motsa jiki na kulob din Glen Driscoll duk za su bar Leicester City.