Leken Sirrin Wayar Maigida 2
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan matsalar leken asirin wayar maigida; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, […]
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo a cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan matsalar leken asirin wayar maigida; da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Mafi kyawun abin yi ga mata:
1. Duk matar auren da tsautsayi yasa ta dauki wayar maigidanta ta duba, sannan ta ga sakonni ko wasu abubuwa da suka bata mata rai, wadanda suka tabbatar mata da cewa maigidanta yana hulda da matan banza, ko wani abu makamancin haka; to mafi kyawun abin da za ta yi shi ne sai ta fara mika al’amarinta ga Allah (SWT) ta hanyar karanta wannan addu’ar bisa koyarwar Manzon Allah (S.A.W):
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un; Allahummar ‘jurniy fiy musibatiy haza, wakhlufliy khairaan minha.
Daga nan in yanayi ya ba ta dama sai ta yi alwallah ta gabatar da sallar nafila raka’a biyu da niyyar neman taimakon Allah (SWT) ya shiryar da ita kuma ya taimake ta kan mafi kyawun hanyar da za ta tunkari wannan al’amari da ya fado mata cikin rayuwar aurenta. Sannan ta ci gaba da ambaton Allah da kyawawan kalamai da tunano girman Jalala da karamcinsa cikin zuciyarta; yin hakan zai tafiyar da fushinta kuma ya nutsar da hankalinta, ta yadda ba za ta yi wani abu ko ta fadi wasu kalamai da za ta zo tana da na saninsu daga baya ba.
2. Abu na biyu shi ne, ya ‘yar’uwa ki sani, ko ma wane dalili ne ya kai ki ga karanta sirrin wayar maigidanki, cikin yarda da amincewar Allah ne kika sami ikon yin haka; don haka sai ki zartar da mafi kyawun al’amari game da abin da Allah (SWT) ya sanar da ke. Wata kila Allah ya sanar da ke halin da maigidanki yake cike don ki dage da yi masa addu’ar shiriya da kuma karin kyautatawa gare shi da fatan Allah ya sa ya tuba ya daina. Don haka ki zama salihar mace ga mijinki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ki rarrashi zuciyarki, ki yi kokarin samun lada a dalilin wannan jarabawa da Ubangiji (SWT) ya kaddaro maki cikin rayuwar aurenki, kar ki yarda ki kwashi zunubi; kar ki nace a kan jin haushi da tsanar maigidanki a dalilin wannan abu da kika karanto; kar ki tsare shi da masifa, zage-zage, cin mutunci da maganganun rashin kunya da rashin ladabi; kar ki rika jin ai ya ci amanarki ko ya yaudareki; wadannan duk ba dabi’un salihar mace ba ne. Ki sani dukkan wani dan’adam ajizine; ya iya sabar Ubangijin da ya halicce shi, kuma ya wadata shi da ni’imomin rayuwa, balle kuma matarsa? Don haka ki yi sauri ki yafe wa maigidanki take yanke, ki yi masa uziri, wata kila abin ya fi karfinsa, wata kila shaidan ne ya rinjayeshi; wata kila ba a cikin son ransa yake aikata wadannan abubuwan ba; wata kila kullum kokarin ya tuba ya daina yake yi a cikin zuciyarsa. Wata kila ‘yan matan ne ke yawan farautarsa. A dalilin hakurin da za ki yi sai ki ga Allah ya yi maki kyakkyawan sakamako, mijinki ya shiryu ya daina aikata duk wasu munanan dabi’u.
3. Abu na uku da uwargida za ta yi shi ne, sai ta auna, ta kuma jinjina cikin zuciyarta da cewa tunkarar shi da maganar ba zai haifar masu da wata babbar matsala ba, to sai ta tunkare shi ta hanya mafi dacewa; in abubuwan da ta gani sun munana sosai sai ta yi masa nasiha, ta fadakar da shi girman zunubin da yake aikatawa. Ta daure kar ta yi masa magana cikin zargi da nuna fushi da fadar bakaken maganganu. In kuma ta lura cewa ko ta tunkare shi da maganar ba zai saurare ta ba, sai dai ma ya karyata maganarta ko ya hau ta da fadan bincike da leken asirin da ta yi masa; wanda hakan zai kara haifar da wasu matsalolin a tsakaninsu, to sai ta daure ta boye wannan al’amari. Sannan ta ci gaba da kyautata masa da yi masa addu’ar Allah ya ganar da shi ya shiryar da shi ya daina aikata dukkan miyagun aiyuka.
4. Abu na hudu mafi dacewa ga matar da ta leko sirrin wayar maigidanta shi ne ta yi kokari daga ranar kar ta kara aikata wannan aiki; ta sa a ranta cewa ta yi na farko ta yi na karshe; ta tuna da cewa duk mai bin diddigin jin sirrin mutane da wuya ya jiyo wa kansa alheri; don haka don samarwa zuciyarta natsuwa da aminci; da kwanciyar hankalinta, sai ta yi dukkan kokari na daina aikata wannan aiki. Musamman in ta tuna cewa ganin wadannan sakonni ba abin da yake haifar mata in banda bacin zuciya da gurbata dangantaka tsakaninta da maigidanta.
5. Abu na biyar shi ne tuba take zuwa ga Allah(SWT); domin yin binciken sirrin dan’uwa musulmi a bayan idonsa, haramun ne kamar yadda ya zo a cikin aya ta 12 cikin Suratul Hujurat; sannan yin hakan cin amanar maigida ne tun da ba da sani ko izininsa aka yi binciken wayar ba; yawancin mata masu binciken sirrin mazajensu za ka taras mazajen nasu ma sun yi masu hani kakkausa a kan su daina bincika masu waya.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.