Lemun ‘Fearless’ ya kara wa masu wasa da motoci da babura karsashi a bikin da Sarkin Gombe ya halarta

An sake farfado da karsashin ’yan wasa wajen baje kolin kwarewarsu a tukin mota.

Lemun ‘Fearless’ ya kara wa masu wasa da motoci da babura karsashi a bikin da Sarkin Gombe ya halarta

Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, rike da tasa robar lemun kara kuzari na Fearless tare da mahalarta a bikin Masu Wasa da Motoci da Babura karo na farko da aka gudanar a Jihar Gombe

Daya daga cikin manyan kamfanonin lemu a Najeriya, Fearless, ya kayatar da mashayansa a taron kungiyar masu wasa da babura da motoci da aka gudanar a Jihar Gombe.

Bikin wanda shi ne irinsa na farko ya nishadantar da masu wasa, da sauran ma’abota lemun a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Taron wanda aka yi wa lakabi da Babban Dandazon Gombe wato ‘Gombe Grand Converge’ shi ne taro mafi girma na wasan dawakai da babura a fadin kasar.

Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, rike da tasa robar lemun kara kuzari na Fearless tare da mahalarta a bikin Masu Wasa da Motoci da Babura karo na farko da aka gudanar a Jihar Gombe

A yayin bikin, an yi hawan Daba da kuma fareti a kan babura domin kayatar da al’ummar Najeriya da kuma Yammacin Afirka baki daya.

An dai kayata bikin ne domin nishadantar da masu sha’awar wasanni wanda aka mayar da hankali a kan hakan fiye da tsarin da aka saba da shi na yau da kullum.

Masu tseren dawakai a bikin da aka gudanar a Gombe

Kamfanin Fearless Energy Drinke ne ya shirya taron wanda ya samu cikakken goyon baya da kuma halartar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, CFR.

Taron ya gudana ke karkashin taken kamfanin na ‘Embrace the Thrill’ wanda ya yi daidai da tsarin wasanni masu ban sha’awa da ke karfafa gwiwar masu ta’ammali da lemun na Fearless da zummar kara musu karsashi na tunkarar wasanni da suke kokwanton ba za su iya kai labari ba.

Wasu abokanan huldar kamfanin lemu na Fearless 

Daga cikin ababen da suka gudana a yayin taron sun hada da wasan da fitaccen mawakin nan, Innocent Idibia wanda aka fi sani da 2 Baba ya yi, wasan da tseren babura, kade-kade, wasanni motsa jiki, tseren mota, kaddamar da dakin karatu, dasa bishiyoyi, da ziyarar ban girma a Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe.

Da yake gabatar da kayayyakin kamfanin ga Sarkin wanda shi ne Uban Taro, Manajan Talla na Kamfanin Rites Foods Limited a yankin Arewa, Emmanuel Agboola, ya ce lemun mai kara kuzari wanda shi ne lamba daya a kasar, ya tanadi tsare-tsare masu habaka nishadi, da karsashi da kuma kuzarin da ake bukata wajen cika-aiki da samun nasara.

Wasu daga cikin ‘yan wasa a bikin wasa da motoci da babura

Ya bayyana cewa amincewar da Sarkin ya yi wa lemun Fearless wata alama ce mai tabbatar da kasancewarsa zakaran gwajin dafi da kuma yunƙurin da aka yi na ganin taron ya kasance abin tunawa yayin da masu amfani da shi da kuma ’yan wasan suka nishadantu wanda wannan babbar alama ce ta ingancinsa ɓangaren kasuwanci.

A nata jawabin, Mataimakiyar Manajan Kamfanin Fearless, Kanyinsola Sangowawa, ta ce kamfanin wanda ya yi kafada-da-kafada da sa’o’insa na duniya , zai ci gaba da tallafa wa wasu ayyuka irisu Babban Dandazon Gombe (Gombe Grand Converge) wanda ya yi daidai da tabarinsu a matsayin kamfanin  lemu mai kara kuzari.

Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, CFR, tare da Manajan Kamfanin Fearless

“Daya daga cikin dalilan da muke daukar nauyin irin wadannan ayyuka ke nan, kuma muna fatan a shekara mai zuwa wani kamfanin lemu mai kara kuzari da zai yi wannan biki da kyau fiye da na mu,” inji ta.

Ta kara tabbatar da cewa, tallafin kamfanin zai kara kusanci tsakanin abokanan hulda da lemun na Fearless wanda ake sarrafawa da wurare na zamani da ke da kaso mai tsoka a bangaren da yake gudanar da kasuwanci.

Masu wasa da babura a yayin bikin

A cewarta, ana iya kwatanta babban matsayi na lemun Fearless da taro ko bukukuwa masu ban sha’awa da kuzari.

A shekarar da ta gabata, kamfanin Fearless ya dauki nauyin kamfanin Fanfaro Autofest da aka yi wa lakabi da “Fearless Edition” domin kara nishadi da kuma burge masu wasan mota da manyan babura a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

A wajen taron, an sake farfado da karsashin ’yan wasa wajen baje kolin kwarewarsu a tukin mota.

Abokan hulda rike da lemun Fearless

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa