Lemun Pepsi ya hada iyaye da malami fada a Saudiyya

Gungun mata sun yi wani malami taron dangi,a makarantar Firamare ta Bakaa da ke kasar Saudiyya, saboda ya kwace wa ’yar su kwalbar lemun Pepsi.. Mai magana da yawun ’yan Sandan Hail, Kanar AbdulAziz Al-Zenaidi, ya bayyana wa Jaridar Arab News cewa, da karfe 10 da 45 na ranar Litinin din da ta gaba ofishin […]

Lemun Pepsi ya hada iyaye da malami fada a Saudiyya
Lemun Pepsi ya hada iyaye da malami fada a Saudiyya

Gungun mata sun yi wani malami taron dangi,a makarantar Firamare ta Bakaa da ke kasar Saudiyya, saboda ya kwace wa ’yar su kwalbar lemun Pepsi..

Mai magana da yawun ’yan Sandan Hail, Kanar AbdulAziz Al-Zenaidi, ya bayyana wa Jaridar Arab News cewa, da karfe 10 da 45 na ranar Litinin din da ta gaba ofishin ’yan sanda na gundumar Bakaa ya samu rahoton daga sashen ilimi na karamar hukuma,game da wasu gungun mata da suka kutsa kai cikin wata sabuwar firamaren ’yan mata. Ana zargin mata da cin mutuncin wasu a makaranta, inda daga bisani suka tafiabin su. Wadanda rikicin ya rutsa das u, sun samu ’yan raunuka.
“An dauki dukkan matakan dasuka kamata, kuma muna neman wadanda suka yi wannan aika-aika, inda za mu gano kosu wane ne, don mu dauki mataki a kansu,” inji Al-Zenaidi.
Wata majiya da ke kusa da malaman makarantar, tabayyana cewa: daya daga cikin malaman ne ya kwace gwangwanin lemun pepsi daga hannun wata daliba, al’amarin da kuwa a cikin tsarin doka yake, domin sashen ilimi ya hana zuwa da lemun kwalba ko na gwangwani a makaranta.”
Malamin da ya cika aikin da doka ta umarce shi, ya cika da mamaki a ranar Litinin din makon jiya, da ya ga gungun mata, wadanda suka hada da iyayen dalibar da ya kwace wa pepsi, inda suka ci mutuncinsa, a gaban sauran malamai da dalibai. Kai hatta malaman da suka yi kokarin sasanta rikicin, su ma sun samu rabonsa na duka.