Leroy Sane ya koma Galatasaray

Kungiyar ta Turkiyya ta dauki dan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Munich.

Leroy Sane ya koma Galatasaray

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray a wannan Alhamis din ta sanar da daukar dan wasan Jamus, Leroy Sane daga Bayern Munich.

Kungiyar ta Turkiyya ta dauki dan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Munich.

Sane mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru uku inda zai rika daukar albashin Yuro miliyan 9 — kwantankwacin Dala miliyan 10.4 — duk shekara kamar yadda kulob din bayyana.

Sane ya buga wa kasarsa ta Jamus wasanni 70, inda kuma ya lashe kofunan Bundesliga guda hudu a Bayern Munich tun bayan raba gari da Manchester City, inda ya dauki Firimiyar Ingila guda biyu.

A kakar bana Sane ya jefa kwallaye 13 a duk gasannin da ya haska, inda ya taimaka wa Bayern lashe gasar Bundesliga bayan ta subuce daga hannunta a kakar bara.

 

AFP