Auren jinsi: Hisbah na bincikar jami’inta a Kano —Daurawa
Jami’in Hisbah da ya halarci taron kungiyar LGBTQ ya yi kira da a ba su dama tare da kare hakkokin mambobinsu
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta fara binciken wani jami’inta da ya alakanta kansa da kungiyoyar ’yan luwadi da madigo da auren jinsi, da aka fi sani da LGBTQ.
Hukumar ta kaddamar da bincike kan lamarin ne bayan bidiyon jami’in ya karade ya karaɗe kafofin sada zumunta, tare da haifar da ce-ce-ku-ce.
Shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jaddada matsayin hukumar na yaki da ’yan luwadi da madigo da dangoginsu, ya na mai nuni da dokar Shari’ar Musulunci ta jihar da ta haramta auren jinsi.
A wani bidiyo da ya yadu, an ga wani wani mutum da ke ikirarin cewa shi jami’in Hisbah ne taron kungiyar LGBTQ, inda yake kira da a ba su dama tare da kare hakkokin mambobinsu.
- Asali da Tarihin Kalandar Musulunci
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Magana Kan Bullar Kungiyar Luwadi Da Madigo A Kano
Da yake tabbatar da cewa wanda ke cikin bidiyon ma’aikacin Hisbah, Sheikh Daurawa ya bayyana, amma ya halarci taron kungiyar ne a kashin kansa, ba da yawun hukumar ba, kamar yadda ya yi ikirari.
Shaikh Daurawa ya ce hasali ma, Hisbah yaki take yi da kungiyoyin ’yan luwadi da aka fi sani da ’yan daudu a jihar.
“Kowa ya san yadda muke yaki da ’yan daudu, mun kai samame tare da rufe wuransu da suka shafi ‘yan luwadi a jihar,” in ji shi.
Daurawa ya kara da cewa Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tunkarar duk wata kungiya ko wani mutum da ke tallata ’yan LGBTQ a jihar, inda ya shawarce su da su bar Kano saboda ba su da wurin buya a jihar.
“Muna sane da cewa wasu kungiyoyi masu zaman kansu a jihar suna inganta harkar LGBTQ. Kuma ba za mu bar su su ci gaba da abin da suke yi ba,” in ji shi.
Daurawa ya ba da tabbacin daukar mataki kan jami’in Hisban da ake yada bidiyon nasa kan zargin.
“Tun daga lokacin mun mika wannan karar zuwa sashin ladabtarwar mu kuma na tabbata za su yi maganinsa yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya yi kira ga jama’a su sanya ido kan ayyukan ’yan LGBTQ a kowane lungu da sako na jihar, domin ’yan kungiyar na nan suna yadawa tare da yaudarar matasa zuwa cikinsu.
A nasa bangaren jami’in Hisban, Idris Ahmed, ya bayyana cewa ya jahilci ma’anar kungiyar ta LGBTQ, inda ya nemi hukumar ta Hisbah ta yi masa afuwa.
“Gaskiya abin da na sani game da wannan kungiya shi ne suna karfafa mata.
“Na sha halartar taron bitarsu, amma ban san ainihin abin da suke tallatawa ba.
“Tsakani da Allah ban san ma’anar kalmar LGBTQ ba.
“Ina ba hukumar Hisbah hakuri kan abin da na yi,” inji shi.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umurci hukumar Hisbah da ta dauki mataki kan kungiyoyin da ke tallata ’yan luwadi da madigo (LGBTQ) da sunan magance rashin daidaiton jinsi a jihar.