Libidin Masarautar Gombe ya rasu

An yi jana’izar Libidin na Gombe a kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe.

Libidin Masarautar Gombe ya rasu

Libidin Gombe

Allah Ya yi wa Libidin Gombe, Alhaji Muhammad Gidado rasuwa bayan shafe shekaru 72 a doron kasa.

An babban rashin a Masarautar Gombe bayan Alhaji Gidado ya rasu dare jiya na Asabar sakamakon fama da ya yi da ’yar gajeruwar jinya.

Rasuwar Libidin rashi ne ba ga Masarautar Gombe kadai ko iyalansa ba rashi ne na jihar Gombe baki daya kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Cikin wata sanarwa da mai magana da da yawun Fadar Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya mika sakon ta’aziyarsa ga masarautar.

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin jigo da ake bukatar shawarwarinsa a daidai wannan lokaci.

Sanarwar ta ce marigayin mutum ne mai hikima wanda shawarwarinsa da jagorancinsa suka kasance masu matukar amfani wanda ya jajirce wajen kiyaye al’adun Masarautar Gombe.

Tuni dai an yi jana’izar Libidin na Gombe a kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Gombe.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara