Libiya ta ce har yanzu ba a gano fursunoni dubu 14 da suka gudu ba

Kimanin fursunoni dubu 14 da suka gudu daga gidajen kurkukun kasar Libiya bayan tawayen da aka yi wa marigayi Shugaba Mu’ammar Ghaddafi a shekarar 2011 har yanzu ba a gano su ba.Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Mohammed Al Cheikh ne y a bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da yake magana kasa […]

Libiya ta ce har yanzu ba a gano fursunoni dubu 14 da suka gudu ba

Sojoji magoya bayan marigayi Shugaba Mu’ammar Gaddhafi da ke tsare a kurkuku. Kimanin fursunoni dubu 14 da suka gudu daga gidajen kurkukun kasar Libiya bayan tawayen da aka yi wa marigayi Shugaba Mu’ammar Ghaddafi a shekarar 2011 har yanzu ba a gano su ba.
Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Mohammed Al Cheikh ne y a bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da yake magana kasa da mako uku bayan da wasu fursunoni 1,200 suka tsere daga wani kurkuku a gabashin birnin Benghazi a lokacin wani tashin hankali.
Mohamed al-Cheikh ya shaida wa jami’an ma’aikatar cewa ma’aikatun cikin gida da na shari’a suna “aiki tare domin dawo da su gidajen kurkuku domin kammala zaman kason da aka yanke musu.”
Cheik ya ce, “Kimanin fursunoni dubu 14 da suke zaman kaso iri-iri har da hukuncin kisan kai da daurin rai da rai har yanzu suna walawa a waje bayan da suka gudu daga kaso. Wannan yana daya daga cikin matsalolin kasar Libya,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran gwamnatin kasae (LANA) ya ruwaito shi yana cewa.
Mahukuntan kasar Libiya na ta faman kokarin dawo da bin doka da oda da kafa rundunar ’yan sanda da ta soja da suka kunshi kwararru, bayan faduwar gwamnatin Ghaddafi.
 A ranar 1 ga Agustan nan ne fursunoni 18 suka gudu daga gidan kurkuku a lokacin da aka kai wani hari ga motar ’yan sandan da a dauko su domin maar da su zuwa kurkuku daga kotu a babban birnin kasar.
Lamarin ya auku ne kasa da mako daya bayan hargitsin da ya jawo fasa gidan kurkukun Benghazi. Kuma a watan Afrilun da ya gabata wasu dauke da makamai sun kai hari ga tawagar ma’aikatan gidan yari a kusa da Tripoli, inda suka kashe wani da ake tsare da shi tare da raunata wasu da dama.