Libya ta zargi Sudan da taimaka wa ’yan tawaye
Mahukunta a Libya sun zargi kasar Sudan da taimakawa ’yan tawayen kasar bayan ta kakkabo wani jirgin saman yakin Sudan da ta ce yana dauke da makamai, a garin Kufra da ke kan iyakar kasashen biyu.Sabuwar gwamnatin Libyar ta zargi Sudan da keta haddinta ta hanyar yin safarar makamai wadanda aka “nufi kaiwa mayaka masu […]
Mahukunta a Libya sun zargi kasar Sudan da taimakawa ’yan tawayen kasar bayan ta kakkabo wani jirgin saman yakin Sudan da ta ce yana dauke da makamai, a garin Kufra da ke kan iyakar kasashen biyu.
Sabuwar gwamnatin Libyar ta zargi Sudan da keta haddinta ta hanyar yin safarar makamai wadanda aka “nufi kaiwa mayaka masu kishin Islama”.
Sudan ta tabbatar da cewa ta tura jirginta, amma ta ce ta yi hakan ne don samar da tsaron hadin gwiwa akan iyakarta da Libyar. Ta kuma ce rashin fahimta ce ta kawo haka, saboda ta yi haka ne don inganta tsaron yankin. Kakakin gwamnatin Sudan al-Sawarmi Khalid ya bayyanawa wata tashar talabijin mai suna Shouruk cewa “jirgin saman bai dauko wasu makamai da nufin bai wa kungiyoyin da ke dauke da makamai ba a Libya, kuma sojojin Sudan ba sa tsoma baki cikin al’amuran kasar”inji shi.
A watan da ya wuce ne Amurka ta zargi kasar Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kai wani hari a asirce a birnin Tripolin kasar Libyan, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13. kasar dai ta fada rikicin siyasa ne shekara uku da suka wuce bayan hanbarar da gwamnatin marigayi Muammar Gaddafi.