Libya za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin CAF

“Hukunci ne da ba a taɓa ganin irinsa ba a fagen wasan ƙwallon ƙafar Afirka.”

Libya za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin CAF

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Libya (LFF) ta ce za ta ɗaukaka ƙara yayin da take ƙoƙarin soke takunkumin da aka ƙaƙaba mata bayan da aka soke wasan da ’yan wasan ƙasar za su buga da Nijeriya a gasar neman shiga gasar cin kofin Afirka a 2025.

Tawagar Super Eagles dai ta ƙi buga wasan ne da aka shirya fafatawa a birnin Benghazi bayan an karkatar da jirginsu zuwa wani filin jiragen sama na daban daga wanda aka tsara za su sauka, aka kuma jibge su a nan ba tare da wani bayani ba har na tsawon kusan sa’o’i 16.

Bayan haka ne kwamitin ladabtarwa na hukumar CAF ya bai wa Nijeriya nasara da ci 3-0 sannan ta ci hukumar LFF tarar dala 50,000.

Muƙaddashin shugaban LFF Abdunnaser Ahmed ya shaida wa BBC cewa “Ba za a iya ba da makin wasa ta haka ba.

“Hukunci ne da ba a taɓa ganin irinsa ba a fagen wasan ƙwallon ƙafar Afirka.”

Ya ƙara da cewa, “Duk wanda ya ƙi buga wasa kafin a soke wasan ya kamata a ɗauke shi a matsayin wanda ya yi rashin nasara.”

Matakin da CAF ta ɗauka ya bar Libya a tsaka mai wuya a gasar, saboda tawagar wasan ƙasar na buƙatar lashe duka wasanninta biyu da suka rage a rukunin D, kuma ta yi fatan abokan karawarta Benin da Rwanda sun gaza samun maki.

Wata sanarwa da hukumar CAF ta fitar ta ce “duk wasu ƙararrakin wasu buƙatun neman sauƙi an yi watsi da su”, amma Ahmed ya tabbatar da cewa LFF za ta ɗaukaka ƙarar har zuwa kotun sauraron ƙararrakin wasanni (CAS) idan hakan ya kama.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Tags