Libya za ta gudanar da zaben majalisa a watan gobe

Gwamnatin kasar Libya ta ce za ta gudanar da zaben ’yan majalisa ranar 25 ga watan gobe duk da matsalolin tsaron da kasar ke ciki.Amma tun da fari gwamnatin ta so ne majalisar ta tafi hutu bayan da ta kammala zaman amincewa da kasafin kudin bana. Jagororin gwamnatin na danganta tashe-tashen hankulan da ke faruwa […]

Libya za ta gudanar da zaben majalisa a watan gobe
Libya za ta gudanar da zaben majalisa a watan gobe

Wata mota da aka lalata a Tripoli, babban birnin kasar Libya Gwamnatin kasar Libya ta ce za ta gudanar da zaben ’yan majalisa ranar 25 ga watan gobe duk da matsalolin tsaron da kasar ke ciki.
Amma tun da fari gwamnatin ta so ne majalisar ta tafi hutu bayan da ta kammala zaman amincewa da kasafin kudin bana. Jagororin gwamnatin na danganta tashe-tashen hankulan da ke faruwa da Janar Khalifa Haftar wanda ake zargi da kitsa juyin mulki. Sai dai ya sha musanta wannan zargin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu mayakan kungiyar Libya National Army (LNA) wanda ake alakantawa da Janar Khalifa, suka kai hari ginin majalisar dokokin da ke Tripoli. Hakan bai zo da wani mamaki ba ganin yadda a baya kungiyar ta taba yin kira da a rusa majalisar. Janar din ya kuma ce kungiyar na kai hare-haren ne don ta karbe iko daga masu kaifin kishin Islama wadanda suka mamaye madafun ikon kasar.
A shekarar 2012 ne jam’iyyar da ba ruwan ta da addini ta lashe zaben ’yan majalisu da aka gudanar a kasar.
Ana ganin wannan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasar bai rasa nasaba da banbancin siyasa da kuma akida tsakankanin’yan siyasar kasar. Masana na ganin zaben majalisar da ake shirin gudanarwa zai iya kwantar da rikicin na dan wani lokaci. Amma wasu na ganin ta hanyar sulhu da sasantawa ne kawai za a iya magance rikice-rikicen da kasar take ciki.
Rikicin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 70, ya kuma haifar da rufe ofishin jakadancin kasashen Saudiyya da Aljeriya. Hakazalika, kasar Faransa ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, takaita aikace-aikacen kamfaninta na mai Total.