Likata zai biya tarar Naira miliyan 16 da rabi saboda ya yi katobara

Wani likita dan kasar benezuela ya haifar da yamutsi a filin jiragen sama na Miami da ke Amurka, inda ya yi barkwanci cewa yana dauke da nakiya samfurin “C-4,” don haka zai biya tarar Dala dubu 90, a cewar lauyansa, Brian Bieber. Manuel Albarado, dan shekara 60, zai biya diyyar asarar da barkwancinsa ya haifar, […]

Likata zai biya tarar Naira miliyan 16 da rabi saboda ya yi katobara
Likata zai biya tarar Naira miliyan 16 da rabi saboda ya yi katobara

Wani likita dan kasar benezuela ya haifar da yamutsi a filin jiragen sama na Miami da ke Amurka, inda ya yi barkwanci cewa yana dauke da nakiya samfurin “C-4,” don haka zai biya tarar Dala dubu 90, a cewar lauyansa, Brian Bieber.

Manuel Albarado, dan shekara 60, zai biya diyyar asarar da barkwancinsa ya haifar, wadda kimarta ya kai Dala $89,172 , wato daidai da kimanin Naira miliyan 16 da rabi. Domin a sanadin wasa da hankalin jami’an kula da filin jirgin sama da ya yi, ya sanya an kashe makudan kudi wajen dakatar da saukar jiragen sama da nemo jami’an ’yan sanda masu kwnace bom.
Yadda al’amarin ya auku kuwa shi ne, da zai hau jirgin saman Abianca zuwa Bogota a ranar 22 ga Oktobar bana, sai wani jami;in tsaro ya tambayi Albarado, wato likita dan kasar benezuela tambayoyin da aka saba yi wa matafiya, shi kuwa fda ya ta shi ba shi amsa, sia ya ce, ‘yabna dauke da nakiya samfurin C-4.’ Kodayake daga bisani ya yi nuni da cewa wasa yake yi, amma tuni jami’an filin jirgin saman suka shiga aikinsu, don ba su dauki al’amarin da wasa ba.
“Ya yi matukar nuna jin kunyar abin da ya aikata. Domin ba shi da nufin tsoratar da kowa. Ya tafka babban kuskure a rayuwarsa,” a cewar Bieber.
Albaro zai biya tarar ne a karkashin wata yarjejeniya da aka kulla ta cewa masu gabatar da kara za su janye tuhumar aikata laifukan da suka hada da bazarana da bom da kulla makirci. Kuma da zarar ya biya wannan tarar, za a kyale likitan ya koma gida, kamar yadda lauyansa ya bayyana.