Likita 1 ke kula da lafiyar ’yan Najeriya 8,300
Likitoci 24,o00 ne suka rage a Najeriya domin kula da lafiyar muutm miliyan 2oo
Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta ce halin yanzu, likitoci 24,o00 ne ke kula da marasa lafiya a Najeriya mai yawan al’umma miliyan 2oo.
Hakan ke nufin duk likita daya zai duba lafiyar mutum dubu takwas da 333 a kasar.
- An yi wa dalibai 8,000 karin alawus din karatu a Nasarawa
- An dakatar da Babban Sakatare kan satar dizel a Ebonyi
- NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Atiku ya ce ’yan Arewa su zabi dan uwansu?
Shugaban Kungiyar Likitocin, Ojinmah Uche, ya ce duk da haka, “Likita daya ne ake da tabbacin zai iya duba marasa lafiya a lokcin da mutum 30,000 ke bukatar kulawa a yankin Kudancin Najeriya.
“A yankin Arewa kuwa, abin ya fi muni ta yadda kimanain mutum 45,o00 za su dogara a kan likita daya domin kula da laifyarsu.
“A wasu yankunan karkara kuma, marasa lafiya kan yi tafiya mai nisam kilomita 30 daga gidajensu kafin su samu ganin likita.
“Wannan yanayi ya sa samun kulawar likita a Najeriya ke kamshin turaren dan goma,” in ji Ojinma.
Ya ce, an samu raguwar likotcin a Najeriya ne sakamakon tsallakawa zuwa wasu kasashe domin aiki da litoci ke yi daga Najeriya.
Shugaban NMA ya bayyana cewa abin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara shi ne mafi karanci, a samu likitoci 23 daga fannoni daban-daban su kula da lafiyar mutum 10,000; amma a Najeriya kusan mutum 10,000 ne ke dogaro a kan likita daya.
Ya bayyana cewa karancin litocin babbar barazana ce, musamman ga kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara.
Ya kuma dangan ficewar likitoci daga Najeriya domin yin aiki a wasu kasashe a kan karancin kudaden kula da bangaren, wahalar karatun likitanci a kasar, rashin aikin yi, rashin albashi mai kyau, rashin tsaro, rikicin kungiyoyin kwararru da sauransu.
Shguaban kungiyar likitocin ya yi wa wanan bayani ne a Abuja a lokcin taron tattaunawa kan tsarin kula da lafiyar mata, wanda aka shirya kan matsalar ficewar likitoci daga Najeriya da kuma tasirinsa ga bangaren lafiyar kasar.
Cibiyar Koyar da Dabarun Harkokin Mulki da Tsara Bukatun Kasa (NIPSS) ce ta shirya taron da halin gwiwar Gamayyar Inganta Lafiyar Yara da na Iyali.
Darakta-Janar na NIPSS da ke Kuru a Jihar Filato, Ayo Omotayo, ya ce a halin yanzu, likitoci ’yan Najeriya ne na uku wajen yawa a tsakanin likitoci ’yan kasar waje da ke aiki a kasar Birtaniya, bayan ’yan Indiya da Pakistan.
A nasa jawabin, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, wanda ya samu wakilcin Daraktan Kula da Marasa Lafiya na Gaggawa, Sydney Ibeanusi, ya ce ficewar kwararrun likitoci daga Najeriya babbar damuwa ce, kuma tana kara samar da matsala a bangaren.
A cewarsa, hanyoyin da za a hana kwarewar likitocin barin kasar sun hada da ci kulla yarjejeniya da wadanda aka horar a cibiyoyi mallakar gwamanti da ke bangaren lafiya, kara kudin karatu a makarantun gwamnati kusa da masu zaman kansu, da kuma bayar da rance ga dalibai, wanda dole su biya bayan kammala karatu, kafin a bari su fice daga kasar.