Likita dan Najeriya ya mutu bayan ya harbu da Coronavirus a Burtaniya
Wani kwararren likita dan asalin jihar Kwara da ke zauna a Burtaniya ya rasu yau Talata 31 ga watan Maris bayan ya harbu da cutar Coronavirus. Likitan mai shekara 68, mai suna Alfa Sa’adu wanda kafin rasuwarsa shi ne Galadiman Pategi ya gamu da ajalinsa ne a bakin aikinsa a wani asibiti da ke Ingila. […]
Wani kwararren likita dan asalin jihar Kwara da ke zauna a Burtaniya ya rasu yau Talata 31 ga watan Maris bayan ya harbu da cutar Coronavirus.
Likitan mai shekara 68, mai suna Alfa Sa’adu wanda kafin rasuwarsa shi ne Galadiman Pategi ya gamu da ajalinsa ne a bakin aikinsa a wani asibiti da ke Ingila.
Kwamishinar masarautun gargajiya a jihar Kwara Aisha Ahman-Pategi, ce ta tabbatar wa kafar sadarwa ta ‘The Cable’ mutuwarsa.
Wani dan uwa ga mamacin ya shaida cewa matar marigayin wacce ita ma likita ce da ke aiki a Burtaniya ta kamu da cutar Coronavirus inda a yanzu take cikin mawuyacin hali.
Kafin rasuwarsa Dakta Alfa Sa’adu, yana aiki ne a Asibitin NHS Trust kana shi ne tsohon babban Daraktan asibitin London.