‘Likita mai hanzari’

Assalamu alaikum Manyan Gobe. Yaya karatu? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Likita mai hanzari”. Labarin ya yi nuni ne ga  yadda hanzari a wani lokaci yake janyo tsautsayi. Taku: Amina Abdullahi An yi wani likita a wani kauye. Likitan ya kasance mai yawan kai ziyara gidajen marasa […]

‘Likita mai hanzari’

Assalamu alaikum Manyan Gobe. Yaya karatu? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Likita mai hanzari”. Labarin ya yi nuni ne ga  yadda hanzari a wani lokaci yake janyo tsautsayi.

Taku: Amina Abdullahi

An yi wani likita a wani kauye. Likitan ya kasance mai yawan kai ziyara gidajen marasa lafiya. Da yake ciwo ya fi tsanani da dare, hakan ya kasance likitan ya fi yin fitar dare domin zuwa duba lafiyar jama’ar kauyen.

Ran nan kamar kullum hadari ya haDu sosai. Matarsa na ganin hakan ta ba shi hakuri da ya dakatar da tafiyarsa har sai ruwan ya wuce. Amma ina! Likita ya dage babu wanda ya isa ya hana shi yin aiki.

Cikin hanzari ya Dauki lemarsa tare da jakar kayan aiki ya fita. Ga shi kuma ba wani abin hawa ne da shi ba.

Aka yi ta yin walkiya da kara kuma aka tafka ruwa kamar da bakin kwarya. Duk da hakan bai canja shawarar ba sai sauri yake yi cikin duhu.  Hasken tocilarsa ne kawai yake amfani da shi wajen haska gabansa.

Bai ankara ba sai ya faDa cikin wani rami da hakan ya sa ya yi targaDe.

Da kyar ya zaro kafar daga cikin ramin. Ga azabar raDaDin ciwo sannan bai samu damar zuwa wurin da ya yi niyya ba.

Da fatan Manyan Gobe za ku rika Daukar shawara da kuma bin komai a tsanake wajen gudanar da kowane irin aiki.