Likita ta mutu bayan ta haifi ’yan uku a Bayelsa

Ya bayyana cewa an garzaya da ita sashin kulawa na musamman (ICU) na Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Yenagoa, inda ta riga mu gidan gaskiya da misalin ƙarfe 2:45 na dare ranar 14 ga watan Afrilu, 2026.

Likita ta mutu bayan ta haifi ’yan uku a Bayelsa

Wata likita mai suna Dakta Ere Ogbachi ta rasu sakamakon matsalolin lafiya da suka taso bayan ta haifi ’yan uku a Jihar Bayelsa.

Wani ɗan uwan mamaciyar mai suna Meshack Sintei ne ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook ranar Laraba. Ya bayyana cewa an garzaya da ita sashin kulawa na musamman (ICU) na Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Yenagoa, inda ta riga mu gidan gaskiya da misalin ƙarfe 2:45 na dare ranar 14 ga watan Afrilu, 2026.

A cewar sanarwar iyalin, ta fara fuskantar matsalolin  ne jim kaɗan bayan ta samu nasarar haihuwar jariran, wanda hakan ya sa aka yi gaggawar kaita sashin kulawa na musamman.

“Ta samu nasarar haifar ’yan uku a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Niger Delta (NDUTH) da ke Okolobiri… sai dai wasu matsaloli sun taso waɗanda suka tilasta mana garzaya da ita sashin ICU a FMC Yenagoa,” in ji sanarwar.

Yayin da suke bayyana lokutan ƙarshe na rayuwarta, iyalin sun ce jami’an lafiya sun yi iyakacin ƙoƙarinsu don ceton ranta a sashin ICU, inda yanayin lafiyarta ta sake taɓarɓarewa cikin sauri.

“Mun kalli yadda take qarfin hali, muna kallon yadda take numfashi da qyar, sannan mun ga yadda rukunin likitoci da sauran qwararru a FMC suka yi ta ƙoƙarin farfaɗo da ita,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ma’aunin iskar oɗygen  na jikinta ya yi ƙasa sosai yayin da ake ƙoƙarin ceto ta. “Injin SpO2 a sashin ICU ya fara karantawa daga 70 zuwa 50, sannan ya koma 0,” in ji shi.

Sintei ya ce, wannan rashi ya girgiza iyalin matuƙa, inda ya bayyana ta a matsayin ƙwararriyar likita mai sadaukarwa kuma mahaifiyar ’yan uku.

“Abin raɗaɗi ne… ƙanwata ƙaunatacciya ta rasu daidai ƙarfe 2:45 na dare ranar 14 ga Afrilu, 2026. Mun rasa babbar jigo, kuma iyalan Sintei suna cikin alhini,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ta kasance “mai jajircewa har zuwa ƙarshen rayuwarta,” sannan ya nuna godiya ga abokai da masu fatan alheri kan goyon bayan da suka nuna musu.