Likita ya saci hodar heroin daga cikin falken kwaya

Yan sandan Rasha sun kama wani Likitan fida a yankin Siberiya ya saci hodar Iblis ta heroin daga cikin falken kwaya. A lokacin da aka kama likitan a garin Bogotolsk, ya sha hodar da ya sata ya yi mankas, kamar yadda ’yan sandan Siberi Krasnoyarsk suka bayyana shafin sadarwarsu.Likitan fidar ya yi wa wani falken […]

Likita ya saci hodar heroin daga cikin falken kwaya
Likita ya saci hodar heroin daga cikin falken kwaya

Yan sandan Rasha sun kama wani Likitan fida a yankin Siberiya ya saci hodar Iblis ta heroin daga cikin falken kwaya. A lokacin da aka kama likitan a garin Bogotolsk, ya sha hodar da ya sata ya yi mankas, kamar yadda ’yan sandan Siberi Krasnoyarsk suka bayyana shafin sadarwarsu.
Likitan fidar ya yi wa wani falken kwaya tiyata, inda ’yan sanda suka bukaci ya fito da kwayoyin da mai laifin ya yi shirin yin safararsu, amma sai bincike ya nuna cewa a lokacin da yake aikin, wasu dauri-dauri na hodar heroin din sun bace.
“Da aka caje likitan fidar, an samu daurin hodar heroin mai nauyin giram biyar. A lokacin da aka tsare likitan, yana cikin maye.” A wani hoton bidiyon da ’yan sandn suka nuna, likitan ya ki amsa tambayoyi.Akwai yiwuwar ya fuskanci hukuncin daurin shekara 15, bisa aikata laifin satar kayan maye da mallakar dimbin kwayoyi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan