Likita ya shawarci iyayen kan rigakafi ga ’ya’yansu

Wani likita a Jihar Kebbi Dokta Abubakar Koko ya shawarci iyayen yara su yi wa ’ya’yansu rigakafin cututtukan da ke addabar yara, musamman a wannan lokaci na zafi. Dokta Abubakar Koko ya bada shawarar ne lokacin da yake jawabi a wurin yekuwar wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga cututtuka masu yaduwa da wata […]

Likita ya shawarci iyayen kan rigakafi ga ’ya’yansu
Likita ya shawarci iyayen kan rigakafi ga ’ya’yansu

Wani likita a Jihar Kebbi Dokta Abubakar Koko ya shawarci iyayen yara su yi wa ’ya’yansu rigakafin cututtukan da ke addabar yara, musamman a wannan lokaci na zafi.

Dokta Abubakar Koko ya bada shawarar ne lokacin da yake jawabi a wurin yekuwar wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga cututtuka masu yaduwa da wata kungiyar Youth Peace Initiatibe ta shirya a binin Kebbi.
Dokta Koko ya ce cututtuka na jawo mutuwar dubban jama’a musamman a lokacin zafi, inda ya ce yekuwar wayar da kan jama’a za ta taimaka wajen rage kamuwa da cututtuka kamar su sankarau da kyanda da sauransu.
Dokta Koko ya ce kungiyar ta shirya yekuwar ne da likitoci da wasu masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya don wayar da kan jama’a game da tsabta da wasu hanyoyin kariya daga kamuwa daga cututtukan da ke yaduwa.
Sai ya yi kira ga wadanda suka halarci yekuwar su maida hankali sosai domin amfana da ababen da za a zayyana a wurin yekuwar.
A jawabin shugaban kungiyar Alhaji Hamza Galadima Zuru ya ce shirin yekuwar an kasa shi gida uku don kowace mazabar Sanata, Kebbi ta Tsakiya a Birnin-Kebbi, sai Kebbi ta Kudu a garin Zuru, sai Kebbi ta Arewa a garin Kangiwa.