Likita yana ƙara wa wata mata girman ɗuwawu ta mutu a Legas

Marigayiyar ta fara haki jim kaɗan bayan da wata ma’aikaciyar jinya ta yi mata allurar a asibitin.

Likita yana ƙara wa wata mata girman ɗuwawu ta mutu a Legas

Wata mata mai shekara 36 mai suna Madam Abiola, ta rasu a lokacin da ake mata tiyatar ƙara girman ɗuwawu a wani asibiti da ke unguwar Lekki a Legas.

An ce marigayiyar ta fara haki jim kaɗan bayan da wata ma’aikaciyar jinya ta yi mata allurar a asibitin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an kama ma’aikaciyar jinya da ta yi wa marigayiyar allura.

Hundeyin ya ce lamarin wanda direban marigayiyar ya kai rahoto a ofishin ’yan sandan ya faru ne a ranar 27 ga Agusta, 2024.

Ya ce, wani direba ya kai rahoto a ofishin ’yan sanda na Maroko cewa da misalin ƙarfe 3:00 na rana, wacce yake yi wa aiki mai shekaru 36 a Diamond Estate da ke unguwar Sangotedo da ke Ibeju-Lekki ta buƙaci ya kai ta wani asibitin da ke Lekki Phase 1. don allurar BBL don ƙara girman ɗuwawu.

“Ya yi iƙirarin cewa da isowar mai asibitin ya umarci wata ma’aikaciyar jinya da ta yi matar allurar, daga nan sai Abiola ta sume ta fara haki, inda ya yi iƙirarin cewa an yi yunƙurin ceto Abiola ne kuma aka garzaya da ita zuwa asibitin Lekki Phase 1 fon duba lafiyarta sai Likitan ya tabbatar da rasuwarta.

“Bisa rahoton, ’yan sanda daga ofishinsu sun ziyarci wurin da aka duba gawar, an ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawarwaki, an kama ma’aikaciyar jinyar,” in ji shi.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu