Likitan bogi da ya auri mata 27 ta hanyar yaudara ya shiga hannu

Mutumin ya kuma amince cewa ya damfari bankuna 12

Likitan bogi da ya auri mata 27 ta hanyar yaudara ya shiga hannu

Likitan bogin da ya auri mata da yawa a Indiya

Wani dan kasar Indiya mai suna Bibhu Prakash Swain, mai shekara 66, da ke tafiya a cikin mota, kwatsam wadansu ’yan sandan musamman suka kewaye shi, inda suka ce tsawon wata takwas suka yi suna nemansa.

Bayan da jami’an tsaro suka yi masa tambayoyi, Bibhu ya yarda cewa yana fitowa ne a matsayin dan yaudara kuma ya auri mata 27 a wasu jihohin Indiya 10.

Jaridar Hindustan Times, ta bayar da rahoton cewa, mutumin ya kuma amince cewa ya damfari bankuna 12 ta hanyar yin katunan cire kudi (ATM) na bogi tare da cin zarafin wadansu mutane da dama.

An kama mutumin ne bayan xaya daga
cikin matansa ta kai kararsa ga ’yan sanda a watan Mayun bara.

’Yan sanda sun ce, Bibhu, wanda ya bayyana kansa a matsayin likita kuma farfesa, yana yunkurin auren mata zaurawa sama da 40 da wadanda suka
samu matsala da danginsu.

“Muradinsa ya yi aure don samun kudi,” inji ’yan sandan.

Bibhu kan fito a matsayin ma’aikacin gwamnati mai samun albashi mai tsoka, kuma waxansu daga cikin matansa sun
hada da farfesoshi da lauyoyi da likitoci da jami’an tsaro.

Ya yi yunkurin yaudarar wacce ta tona masa asiri ne ta hanyar shiga shafin Intanet don yin soyayya da ita yayin da ya yi ikirarin shekarunsa 51.

Hukumomin kasar sun yi qiyasin cewa, zai iya tara kudi har KSh miliyan 1.5 na kasar (kimanin Naira miliyan 5.5) daga matan da ba a san ko su wane ne ba.

’Yan sanda sun ce, mutumin yana
zaman lafiya da matan, a kwanaki kaxan bayan aure, daga bisani sai ya nemi uzuri don karvar kudi ko gwalagwalai ko zinare na matan da nufin yana cikin gaggawar buqatar kudi.

Bayan ya samu abin da yake so, sai ya koma wani yankin. Tunaninsa matan zawarawa ne ko wadanda aurensu ya mutu da suka sake yin aure a cikin al’umma masu ra’ayin mazan jiya, kuma ba za su iya kai shi kara wajen ’yan sanda ba saboda tsoron kada su sake zama zawarawa.

’Yan sandan sun tabbatar da cewa, Bibhu kwararren masanin fasaha ne, ya yi aure a 1978 kuma yana da ’ya’ya uku.

Ya canza garuruwa bayan ya saki matarsa, sai ya fara gabatar da kansa a matsayin likita ko farfesa yana yaudarar mata.