Likitan bogi ya shiga hannu bayan shekara tara
Wani babban jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ke aiki a matsayin likita na tsawon shekara tara ya shiga hannun ’yan sanda bayan da aka gano ya saci lasisin aikin likita na abokinsa ne. Mutumin mai suna Martins Ugwu babban jami’in lafiya ne na biyu da ke matakin albashi na 13, kuma an gano […]
Wani babban jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ke aiki a matsayin likita na tsawon shekara tara ya shiga hannun ’yan sanda bayan da aka gano ya saci lasisin aikin likita na abokinsa ne.
Mutumin mai suna Martins Ugwu babban jami’in lafiya ne na biyu da ke matakin albashi na 13, kuma an gano ya yi sojan gona ga abokinsa Dokta George Daniel, wanda yake aiki a Jos ta Jihar Filato, kamar yadda majiyarmu ta gano.
An ruwaito cewa ana zargin Mista Ugwu ya sace lasisin abokinsa ne wanda ya yi masa abota a lokacin bikin aurensa a shekarar 2006. Dukkan mutanen biyu sun fito ne daga garin Orukpa da ke karamar Hukumar Ogbadibo da ke Jihar Benuwai.
Wanda ake zargin yana daf da za a yi masa karin girma zuwa Mataimakin Darkta a Cibiyar Yaki da Cututtuka maso Yaduwa a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, kuma ya fara aiki ne da ma’aikatar tun shekarar 2006 da sunan Dokta George Dabidson Daniel, kafin Hukumar Kula da Likitoci ta Najeriya (MDCN) ta gano sojan gona yake yi kuma aka kama shi a ranar Alhamis din makon jiya.
Kama Ugwu ya biyo bayan binciken da Hukumar MDCN, wadda take da alhakin yi wa daukacin likitocin Najeriya rajista tare da kula da ayyukansu ta gudanar inda ta gano akwai Dokta Daniel biyu masu suna daya amma hotunansu sun bambanta.
Wani abin mamaki Ugwu yana cikin wani kwamitingwamnati da ya gana da ayarin ma’aikatan lafiya 200 da suka dawo daga kasashen Saliyo da Guinea inda suka je aikin sa-kai don yaki da cutar Ebola a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka a makon jiya a Abuja.