Likitan da ake zargi da yanke ƙodar mara lafiya ya koma ‘mahaukaci’ a ofishin ’yan sanda
Yanzu haka an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos
Noah Kekere, likitan nan da ake zargi da yanke kodar wata mara lafiya a Jos, ya koma mahaukaci da rana tsaka lokacin da yake tsare a hedkwatar ’yan sandan Jihar Filato.
An kama Noah ne ranar Laraba, bayan wani rahoton korafi da aka kai asibitin Nasarawa Gown bisa zargin cire kodar wata mata yayin wani aikin tiyata a shekara ta 2018.
- Mutanen da suka rasu a girgizar kasar Maroko sun haura 2,000
- Faransa na kokarin afka mana da yaki – Sojojin Nijar
Tun da farko dai Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta tabbatar da kama wanda ake zargi da yanke kodar ba bisa ka’ida ba.
Sai dai lokacin da ake bincike a kan shi a hedkwatar ’yan sandan a ranar Asabar, Noah ya fara nuna alamun tabin hankali.
Hakan ce ta sa aka saka masa ankwa sannan aka garzaya da shi sashen kula da masu matsalar kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) domin a duba lafiyarsa.
Wata majiya daga hedkwatar ‘yan sandan ta ce an garzaya da wanda ake zargin asibiti ne lokacin da ya fara nuna alamun hauka, yana yayyaga kayan jikinsa a ofishin ’yan sanda.
Wata majiya daga asibitin ita ma ta tabbatar da cewa tuni suka karbi mutumin kuma yanzu haka yana can ana kula da shi.
Wakilinmu ya rawaito cewa tuni ’yan sandan kwantar da tarzoma suka yi wa sashen da aka kwantar da likitan a asibitin kawanya.
Da aka tuntubi Kakaki Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar wakilinmu ba a kan lamarin.