Likitan Ebola ya mutu a Saliyo
A kasar Saliyo, cutar Ebola ta yi ajalin wani likitan da ke jagorantar yakin da annobar cutar a kasar, ’yan kwanaki kadan bayan harbuwarsa da cutar.Gidan rediyon BBC ya ruwaito cewa likitan mai suna Sheikh Umar Khan ya kamu da cutar ne lokacin da yake jinyar wasu da ke fama da ita a garin Kenema, […]
A kasar Saliyo, cutar Ebola ta yi ajalin wani likitan da ke jagorantar yakin da annobar cutar a kasar, ’yan kwanaki kadan bayan harbuwarsa da cutar.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito cewa likitan mai suna Sheikh Umar Khan ya kamu da cutar ne lokacin da yake jinyar wasu da ke fama da ita a garin Kenema, garin da ke fama da annobar cutar.
Ministar Lafiyar ta kasar Saliyo, Miatta Kargbo ta jinjina wa marigayin, tana cewa ya isa gwarzo, lokacin da ta samu labarin cewa ya harbu da cutar.
Cutar ta Ebola dai tana ci gaba da watsuwa a kasashen Afirka ta Yamma inda a makon jiya aka samu bayyanar mutum daya da cutar ta kashe a nan Najeriya, lamarin da ya tilasta hukumomin lafiya kebe mutum 59, da ake kyautata zaton sun yi mu’amala da mutumin dan kasar Liberiya.
Mutumin ya mutu ne ranar Juma’a a Legas, bayan da ya iso kasar ta jirgin sama daga Liberiya.
An kebe mutanen ne a yunkurin tabbatar da cewa ba su harbu da kwayar cutar ta Ebola mai saurin yaduwa da saurin kisa ba.
A wata hira da BBC, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ya ce suna daukar matakan da suka dace don ganin sun dakile cutar.