Likitan Sardauna ya rasu

A ranar Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa likitan marigayi Sa Ahamdu Bello Firimiyan Arewa na farko, Dokta Abdulmumin Ibrahim Atta rasuwa.Marigayi Dokta Atta wanda shi ne likita na biyu da ya fito daga yankin Arewa a bayan Dokta R. B. Dikko.Likita Abdulmumini mai shekara 97 ya rasu ne a gidansa da […]

Likitan Sardauna ya rasu
Likitan Sardauna ya rasu

A ranar Litinin da ta gabata ne Allah Ya yi wa likitan marigayi Sa Ahamdu Bello Firimiyan Arewa na farko, Dokta Abdulmumin Ibrahim Atta rasuwa.
Marigayi Dokta Atta wanda shi ne likita na biyu da ya fito daga yankin Arewa a bayan Dokta R. B. Dikko.
Likita Abdulmumini mai shekara 97 ya rasu ne a gidansa da ke kan Titin Gobir daura da Titin Gobarau a GRA din Unguwar Rimi, Kaduna.
An yi masa sallar janaza da misalin karfe 2:00 na rana inda Babban Limamin Masallacin Juma’a na Almannar, Sheikh Muhammad Tukur Almannar ya jagoranta.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci sallar janazar akwai Jakadan Najeriya na farko a kasar Kyuba Ambassada Abdullahi Atta da tsohon Manajan Bankin Unity  Alhaji Falalu Bello da Ambassada Adamu Muhammad da tsohon Gwamnan soja na jihohin Kwara da Kano, Iya Mashal Mohammed Ndatsu Umaru wanda surukin marigayin ne.
Sauran su ne tsohon Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Laftana Janar Mohammed Inuwa Wushishi da tsohon shugaban Jam’iyyar ANPP na Kaduna kuma surukin marigayin, Sanata Mohammad Lawal Aliyu.
Marigayi Abdulmumin ya rasu ya bar ’ya’ya uku da suka hada da Dokta Ibarahim Atta da jikoki masu yawa. Kuma an binne shi ne a makabartar Titin Isa kaita a Unguwar Sarki, Kaduna.
Tuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikie da sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin wanda ya bayyana da fitaccen ma’aikacin da ya bauta wa kasarsa tare da bayar da gagarumar gudunmawa a bangaren kiwon lafiya.