Likitoci 2 da abokansu sun rasu a hatsarin mota Sakkwato

Dakta Anas Chika da Dakta Abubakar Liman Shehu sun rasu ne tare da wasu abokansu hudu bayan motarsu ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

Likitoci 2 da abokansu sun rasu a hatsarin mota Sakkwato

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki

Wasu likitoci biyu matasa da ke aiki a Asibitin Kwararru na Jihar Sakkwato sun rasu a tare a hanyar Boɗinga-Yabo da ke Jihar.

Dakta Anas Chika da Dakta Abubakar Liman Shehu sun rasu ne tare da wasu abokansu hudu bayan motarsu ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

Da yake tabbatar da lamarin Shugaban Asibitin Kwararru na Jihar Sakkwato, Dakta Attahiru Isa, ya bayyana cewa Dakta Shehu na daga cikin manyana liman asibitin.

Ya ce marigayan, “mutanen kirki ne masu sauƙin kai, tare da su muka yi Sallar Juma’a. Haƙiƙa mun girgiza da wannan rashi, amma mun fawwala wa Allah. Muna rokon Allah Ya sanya su a Alh’janna ya ba wa iyalansu haƙurin jure wannan rashi.”

Wani abokin aikinsu, Dakta Tijjani Farin, ya ce yana tare da su a wurin tantance ma’aikata da gwmanatin jihar, sa’o’i kaɗan kafin rasuwar tasu.

Ya ce, “har kofin shayi na ba ɗaya daga cikinsu.”

Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) Reshen Jihar Sakkwato, Dakta Farouk Kabiru, ya bayyana cewa likitocin biyu matasa ne, kuma jihar za ta yi kewar rahsinsu da kuma irin gudunmawarsu wajen kula da lafiyar al’umma.