Likitoci 59 Sun Ajiye Aiki A Jihar Nasarawa

A cikin kwanaki biyu kacal likitoci fiye da 25 sun gabatar da wasiƙun ajiye aiki.

Likitoci 59 Sun Ajiye Aiki A Jihar Nasarawa

Likitoci

Likitoci 59 da ke aiki da Asibitin ƙwararru na Dalhatu Araf (DASH) a birinin Lafiya da ke Jihar Nasarawa, sun ajiye aiki.

Likitocin sun bar ayyukansu ne bisa rashin cika waɗansu yarjeniyoyi da suka haɗa da alawus alawus ɗinsu da rashin kyautata musu tsarin aikinsu da gwamnati ta yi.

Bayanai sun ce ma’aikatan lafiya su 59 sun bar aiki ne a cikin watanni uku kacal da suka gabata.

Binciken da Aminiya ta gudanar, ta gano cewa a cikin likitoci 20 sun tafi kasar Saudiyya ne, yayin da 39 suka yi murabus saboda rashin kyan tsarin aikin, a cewarsu.

Wakilinmu ya gano cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, manyan asibitoci mallakin gwamnatin jihar Nasarawa na fama da rashin kyan asibitoci, mummunan yanayi, sai kuma yawan tafiya yajin aiki, da zanga-zangar lumana da kuma murabus daga ma’aikatar lafiyar jihar.

Ya kuma gano cewa lamarin ya ƙara ta’azzara ne bayan murabus ɗin din da likitoci sama da 50 daga ma’aikatar lafiyar jihar suka yi a tsakanin watan Janairu zuwa Maris a 2024.

Wani babban jami’in gwamnati a sashen gudanarwa na DASH da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa wakilinmu cewa, sun samu wasiƙun ajiye aiki sama da 25 daga likitoci a cikin kwanaki biyu.

Shugaban kungiyar likitoci ta kasa reshen jihar Nasarawa, Dokta Yakubu Adeleke, ya bayyana cewa tun a shekarar 2022 suke bai wa gwamnati shawarar cewa ta gaggauta biya musu buƙatunsu da suka shafi walwalarsu, da kyautata musu tsarin aikinsu, amma duk ƙoƙarin da aka yi ya ci tura.

Ya ce, “Likitoci a Jihar Nasarawa na cikin wani hali na rashin ci-gaba. Babu tsarin samun ƙarin girma”.

“Wasu likitocin sun shafe shekaru takwas suna aiki ba tare da sun sami ƙarin girma ba.”

Dokta Adeleke ya ce, murabus ɗin din da likitocin suke yi a baya-bayan nan zai ƙara matsin lamba kan tsarin kiwon lafiyar jihar.

Wasu daga cikin likitocin da suka zanta da manema labarai a jihar, sun ce hakurin su ya ƙare.

Kwamishinan lafiya a Jihar Nasarawa, Dokta Gaza Gwamna, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara aiwatar da shirin kyautata albashi da tsarin aikin likitoci a jihar.

Ya yi kira ga sauran likitocin da su kwantar da hankalinsu, ya kuma kara da cewa sun fara aikin ɗaukar ma’aikata domin cike guraben waɗanda suka tafi.

Wakilinmu ya gano cewa tasirin murabus ɗin din likitocin ya fara bayyana a asibitin kwararru na Dalhatu Araf, yayin da ya ga marasa lafiya jingim suna layin jira na tsawon sa’o’i kafin su sami damar ganin likita.