Likitoci 88 sun ajiye aiki a Jihar Kogi

Kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jihar Kogi ta ce likitoci 88 ne suka ajiye aiki a jihar bisa radin kansu a zamanin mulkin Gwamna Yahaya Bello, inda suka tafi neman guraben aikin da suka fi na jihar gwabi. Kungiyar ta shawarci gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa wajen dakile wannnan yanayi da ke sa likitocin […]

Likitoci 88 sun ajiye aiki a Jihar Kogi

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello

Kungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jihar Kogi ta ce likitoci 88 ne suka ajiye aiki a jihar bisa radin kansu a zamanin mulkin Gwamna Yahaya Bello, inda suka tafi neman guraben aikin da suka fi na jihar gwabi.

Kungiyar ta shawarci gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa wajen dakile wannnan yanayi da ke sa likitocin ajiye aikinsu a jihar.

Shugaban kungiyar, Dokta Kabiru Zubairu ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata a wata takarda da ya aike wa Gwamnan, domin taya shi murnar cika shekara uku a gadon mulkin jihar ta Kogi.

A cewarsa, “A karkashin wannan gwamnati, likitoci 88 ne suka bar aiki a Ma’aikatar Lafiya ta jihar. Tun da farko likitoci 79 ne suka bar aikin, a yayin da kuma a kwanan nan wadansu 9 suka bari, bayan da suka samu wasu guraben aikin na daban a wasu wurare.”

Dokta Zubair ya ce likitoci da sauran ma’aikatan lafiya sun kasance ginshikin samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma a ko’ina a duniya.

“Ya kamata a dauki ingantattun matakai, kamar biyan bashin albashin baya a kammale ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da ba a biya su ba, a kuma biya tsarin albashi da alawus-alawus na CONMESS, a kara girma ga wadanda suka cancanta, a kara musu matakan albashi. Wadannan matakai da sauransu, za su taimaka wajen jawo hankalin likitocin su daina barin aiki a jihar.

“A lokacin da kake shiga shekara ta 4 ta mulkinka, Kungiyar Likitoci ta Najeriya, a matsayinta na jigon kula da lafiyar al’umma, a shirye take ta hada kai da gwamnatinka domin gyara kura-kuran da aka yi a baya a sashen lafiya a Jihar Kogi,” inji Dokta Zubair.