Likitoci a Kanada sun ki amincewa da karin albashi

Likitocin da ke aiki a birnin kuebec na kasar Kanada sun girgiza duniya bayan da suka ki amincewa a kara musu albashi. Su dai wadannan likitoci na birnin kuebec sun ce sun ki amincewa da karin albashi ne domin a mika kudin wurin kula da lafiyar masu larura kamar yadda kafar labarai ta BBC ta […]

Likitoci a Kanada sun ki amincewa da karin albashi


Likitocin da ke aiki a birnin kuebec na kasar Kanada sun girgiza duniya bayan da suka ki amincewa a kara musu albashi.

Su dai wadannan likitoci na birnin kuebec sun ce sun ki amincewa da karin albashi ne domin a mika kudin wurin kula da lafiyar masu larura kamar yadda kafar labarai ta BBC ta ruwaito.

Wata yarjejeniyar shekara takwas da aka sanya wa hannu a watan Fabrairu za ta bai wa likitoci kusan dubu 20 damar samun karin daga kashi 1.4 zuwa kashi 1.8 a kowacce shekara.

Hakan na nufin, yankin na kuebec wanda ke yin tallafi a albashin likitocin, zai ware musu karin Dala biliyan 1.2 zuwa shekarar 2023.

kungiyar kwadago da ke wakiltar likitocin, wacce ta sa gwamnati yin karin albashin, ta ce matakin wani adalci ne a gare su.

Sai dai ba dukan likitocin ne suka ji dadin wannan karin albashi ba domin fiye da 700 daga cikinsu sun sanya hannu a kan wata takarda ta kungiyar Likitocin ta Medecins kuebecois Pour le Regime suna masu cewa ba sa bukatar karin albashin.

A cewarsu, ya kamata a yi amfani da kudin ne wurin yi wa marasa lafiya da sauran masu larura magani.

A cewarsu, “Mu likitocin kuebec, muna so a soke karin albashin da aka yi mana sannan a yi amfani da kudin wajen inganta rayuwar ma’aikatan lafiya da marasa lafiyar kuebec,” inji wata sanarwa da suka fitar.

Makonni kadan bayan fitar da wannan sanarwa, an samu karin likitoci 250 da ke so a soke karin albashin. Kuma akwai kimanin likitoci dubu 20 a yankin na kuebec.

Wannan bukata da suka shigar ta son inganta lafiyar masu larura tana zuwa ne a daidai lokacin da ake tsananta bincike a kan harkokin kiwon lafiya a kasar.

A shekaranjiya Laraba, sakamakon wani bincike da Hukumar Lafiya da Walwalar Jama’a ta kuebec mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa an ninka albashin likitocin yankin daga 2005-15, yayin da lokacin da likitocin ke bai wa marasa lafiya ya ragu.

A gefe guda kuma, ma’aikatan jinya a kuebec na fafutikar ganin an inganta yanayin aiki da kuma albashinsu.