Likitoci da Gwamnati na ganawar sirri

Kungiyar likitoci (NARD) na shirin shiga yajin aiki ranar 17 ga Agusta.

Likitoci da Gwamnati na ganawar sirri

Gwamnatin Tarayya na yin wata ganawar sirri da kuniygar likocin Najeriya ta NARD domin dakatar da yajin aijin da ma’aikatan lafiya ke shirin farawa.

Ganawar tsakanin Ministan Kwadago Chris Ngige da shugabannin NARD na zuwa ne bayan kungiyar ta yi barazanar komawa yajin aikin da ma’aikatan lafiya suka dakatar.

Kungiyar ta Dakta Aliyu Sokumba na zargin gwamnatin da cika alkawuran da ta yi a kan bukatunta da suka sa ta fara yajin aikin a wancan lokacin.

A karshen makon jiya ne kungiyar ta ba wa gwamnatin wa’adin ranar 17 ga watan Agusta ta cika alkawuran ko kuma ma’aikatan lafiya su shiga yajin aikin.

Likitocin na neman gwamnati ta samar wa likitocin da ke jinyar masu cutar coronavirus isassun kayan kariya, ta kuma biya su alawus dinsu na aikin kamar yadda aka tsara.

Suna kuma bukatar gwamnai ta dauki nauyin karon ilimin likitoci da kuma biyan likitocin jihohi bambancin da ke tsakanin albashinsu da na takwarorinsu da ke aiki a Gwamnatin Tarayya.

A ganawarsa da ‘yan jarida bayan taronsu na makon jiya, shugaban NARD ya ce suna bukatar “Nan take a biya bashin cikon sabon albashin likitocin da sauran ma’aikatan lafiya”.

Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tarayya su yi cikakken bincike a kan rashin biyan hakkokin likitocin da suka rasu a bakin aiki ga magadansu.

“Sannan a biya cikakken diyya ga ‘yan kungiyar da ke aiki a jihohi”, kuma a yi wa ma’aikatan lafiya inshorar rayuwa, inji shugabannin kungiyar.

Sai kuma batun biyan likitoci wadataccen albashi kamar yadda aka yi musu alkawari.

Sun kuma bukaci Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal, Farfesa Henry Ugboma ya sauka daga mukaminsa nan take saboda zargin almundahana da tsaurin ido.

Sa’annan a dawo da shugabannin reshen kungiyar na asibitin karkashin jagorancin Dakta Solomom Amadi, wadanda aka dakatar, ba tare da wani sharadi ba.

NARD ta ce taron nata ya yi nazarin yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen biyan bukatun ‘ya’yanta tun bayan janye yakin aikin da suka shiga saboda matsalolin a baya.