Likitoci sun bukaci a dage komawa makaranta

kungiyar Likitocin ta Najeriya ta yi soki matsayin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta dauka na sanya ranar 22 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a sake bude makarantun sakandare da firamare da ke kasar nan.kungiyar ta bukaci a sake dage komawa makarantun har zuwa karshen shekara a wani mataki da ta kira […]

Likitoci sun bukaci a dage komawa makaranta
Likitoci sun bukaci a dage komawa makaranta

kungiyar Likitocin ta Najeriya ta yi soki matsayin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta dauka na sanya ranar 22 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a sake bude makarantun sakandare da firamare da ke kasar nan.
kungiyar ta bukaci a sake dage komawa makarantun har zuwa karshen shekara a wani mataki da ta kira na kauce wa yaduwar cutar Ebola a kasar nan.
kungiyar ta yi zargin cewa an sanya siyasa cikin lamarin domin a ganinta bai kamata a koma karatu ba, har sai an tabbatar da cewa babu sauran mai dauke da kwayar cutar a Najeriya.
Shugaban kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Kano Dokta Sharfuddeen Mashi a hirarsu da gidan rediyon BBC Landan, ya ce manyan jami’an ilimi na jihohi da suka yanke wannan shawarar tare da Ministan Ilimi, mutane ne da aka nada a kan mukamansu, don haka dole ne su taka rawa da wadanda suka nada  su ke so.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya