Likitoci sun cire idon mara lafiya ‘bisa kuskure’ yayin tiyata
Tuni dai likitan da ya yi aikin ya cika wandonsa da iska
Likitoci da ke aikin tiyata a wani babban asibitocin kasar Slovakia sun cire lafiyayyen idon wani mara lafiya a maimakon mara lafiyar yayin wata tiyata, inda a yanzu ya koma makaho gaba daya.
Kamfanin dillancin labarai na TARS ne ya rawaito hakan a ranar Laraba.
- Me Dokar Zabe ta ce kan canza ’yan takarar ‘wucin gadi’?
- Na damu matuka da yadda Sanatoci ke ficewa daga APC – Abdullahi Adamu
Sai dai rahotanni sun ce tuni likitan, wanda ke aiki da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Bratislava, da ya aikata katobarar ya cika wandonsa da iska.
Asibitin dai a sakamakon haka ya zaunar da iyalan mutumin domin ba su shawarwari domin su rage radadin halin da aka jefa su a ciki.
A cewar TARS, tuni hukumomin lafiyar kasar suka fara gudanar da bincike don gano yadda aka yi ma lamarin ya faru tun da farko.
Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da bangaren lafiyar kasar ta Slovakia ke fama da yajin aiki.
Ko a makon da ya gabata sai da Kungiyar Likitoci ta Kasar (LOC) ta ce akwai mambobinta kimanin 3,000 da suke a shirye su ajiye aikinsu matukar ba a yi musu karin albashi tare da inganta yanayin aikinsu ba.
Kasar dai na fama da kamfar likitoci inda suke fice wa zuwa kasashen waje, musamman Jamhuriyar Czech da Austria, kuma annobar COVID-19 ta dada ta’azzara lamarin.
(NAN)