Likitoci sun cire tsakuwa guda 420 a kodar majinyaci

Wasu likitoci a kasar China sun cire tsakuwa 420 a kodar wani marar lafiya, kamar yadda kafar yada labaran Birtaniya ta Daily Sun ta bayyana. Mutumin mai suna, He, an kwashe tsawon sa’o’i biyu wajen ceto rayuwarsa a wani asibiti da ke lardin Zhejiang na kasar. Inda suka danganta faruwar hakan da yadda majinyaci ya […]

Likitoci sun cire tsakuwa guda 420 a kodar majinyaci
Likitoci sun cire tsakuwa guda 420 a kodar majinyaci

Wasu likitoci a kasar China sun cire tsakuwa 420 a kodar wani marar lafiya, kamar yadda kafar yada labaran Birtaniya ta Daily Sun ta bayyana.

Mutumin mai suna, He, an kwashe tsawon sa’o’i biyu wajen ceto rayuwarsa a wani asibiti da ke lardin Zhejiang na kasar. Inda suka danganta faruwar hakan da yadda majinyaci ya nace wa cin wani nau’in abinci mai lakabin tofu musamman ma saboda yadda yake ba ya shan ruwa yadda ya kamata.
Sai dai ba wannan ba ne karon farko da ka cire wa majinyacin tsakuwa a ciki, shekara 20 da suka wuce ma an samu irin hakan, inda a lokacin aka cire masa kwaya 10.
Likitan da ya jagoranci aikin da aka yi masa ranar Juma’ar da ta wuce, ya ce duk tsawon shekarun da ya kwashe yana aikin likita bai taba ganin mutumin da aka cire wa tsakuwa da suka kai yawan na Mista He ba.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta