Likitoci sun cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin kilo 35 a ciki

Likitoci sun cire wani kullin kumburi mai nauyin kilo 35, al’amarin da ya sanya matar da ke da wannan cuta ta rika zaton ta dauki juna biyu. Kafin likitar asibitin kasimi, Dokta Kawthar Mansour, wata kwararriya kan harkar kula da lafiya mata masu juna biyu, ta gano cewa matar na da nauyin kilo 103, amma […]

Likitoci sun cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin kilo 35 a ciki
Likitoci sun cire wa wata mata kullin cuta mai nauyin kilo 35 a ciki

Likitoci sun cire wani kullin kumburi mai nauyin kilo 35, al’amarin da ya sanya matar da ke da wannan cuta ta rika zaton ta dauki juna biyu. Kafin likitar asibitin kasimi, Dokta Kawthar Mansour, wata kwararriya kan harkar kula da lafiya mata masu juna biyu, ta gano cewa matar na da nauyin kilo 103, amma bayan an yi mata aikin fida, nauyinta ya koma kilo 68. Likitiyar ta ce wannan shi ne mafi girma da nauyin kullin cuta da ta taba gani a an cire wa mara lafiya. Matar da ta yi fama da laulayi a sanadiyyar nauyin cutar da ta kumburo daga cikinta, wadda shekarunta ba su wuce 31, ta isa asibitin ne da tulelen cikinta, inda take zaton tana da ciki dan watan shida, kamar yadda likitar ta bayyana wa jaridar GulfNews. Da aka dauki hoton cikin, sai aka gano cewa kullin ciwo ne a jikinta. Don haka suka ba ta shawara kan lallai ta bari a cire mata shi. A ranar Alhamis din makon jiya aka yi mata aiki, inda aka ciro wannan kullin da ya kumbura mata ciki. Ana kammala aikin, sai nauyin jikinta ya yiwo kasa daga kilo 103 zuwa 68. Wadannan nauyi da ya taru a cikin matar an kimanta kwatankwacinsa da nauyin jarirai 10. Kafin a gano ciwon da ke damun wannnan matar sai da likitoci suka ba ta shawarar ta riga zuwa ana duba lafiyarta da zarar ta kusa haihuwa. Bincike da kididdiga sun nuna cewa mata da dama na fama da wannan cuta, wadda idan har ba a dauki amtaki cikin sauri ba, za ta iya rikidewa, ta zama cutar daji.