Likitoci sun ciro karafuna 38 daga cikin wani mutum

Likitoci sun ciro karafuna 38 daga cikin wani mutum, wadanda mayen karfe ya tattare su wuri guda. Likitocin a Babban Asibitin Gwamnati na Rajib Gandhi a Chennai birnin Jihar Tamil Nadu da ke Yamma maso Gabas na kasar Indiya ne suka yi wannan aiki. Sun yi wa wani marar lafiya mai suna Jayakumar mai shekara […]

Likitoci sun ciro karafuna 38 daga cikin wani mutum

Likitoci sun ciro karafuna 38 daga cikin wani mutum, wadanda mayen karfe ya tattare su wuri guda.

Likitocin a Babban Asibitin Gwamnati na Rajib Gandhi a Chennai birnin Jihar Tamil Nadu da ke Yamma maso Gabas na kasar Indiya ne suka yi wannan aiki. Sun yi wa wani marar lafiya mai suna Jayakumar mai shekara 52 tiyatar minti 45 wajen cire karafunan da ya hadiye.

Karafunan da Jayakumar ya hadiye sun hada da makullai da tsabar kudade da layin waya SIM.

Likitocin sun ce, bayan karafunan da suka fitar sun ciro rezar feke fensuri da mayen karfe da ya rike sauran karafuna a cikinsa.

Likitocin asibitin sun ce, idan ba su yi wa wannan marar lafiya tiyata ba zai iya rasa ransa.

Likitan da ya jagoranci tiyatar Dokta A.R. Benkateswaran, ya ce  da ba a yi hanzarin cire karafunan da suke cikin mutumin ba, da ya haddasa masa ciwon hanji wanda daga karshe na iya zama ajalinsa.

Likitocin asibitin sun bi matakan da suka dace sama da kwana biyu sannan suka ciro karfuna 22 daga cikin Jayakumar yayin da a cikin kwana daya na gaba suka ciro abubuwa 18 a cikinsa.

Likitocin sun ce, mafi karancin abin da suka ciro shi ne mai tsawon santimita 2 yayin da wasu kuma suka manne a mayen karfe duk a cikinsa.

Da farkon karfen da aka fara ganowa shi ne lokacin da yake fama da cutar tabin kwakwalwa don yi masa magani shekara uku da suka wuce.

Wani likita da yake asibitin Dokta Jayanthi Rangarajan, ya ce wannan lamari da ya samu marar lafiyar ya hadu ne da wani gurbi da  ke da mayen karfe inda ya rika tattara sauran karfuna a cikinsa.

Jayakumar ya fara ne da ciwon ciki, sai aka yi masa hoton cutar da ke damunsa, a nan ne aka gano karfunan da ke cikin suna da yawa.

Dokta A.R. Benkateswaran, ya kara da cewa, a mako na uku na watan Fabrairu ne likitocin da suka fara duba Jayakumar suka turo shi asibitin da aka yi nasarar yi masa wannan tiyata.

Iyalan Jayakumar sun ce, ba su da wata masaniya game da hadiyar karafuna da yake yi.

Bayan binciken likitocin sun gano karfuna dunkule a waje guda a cikinsa.

An dai ciro wa Jayakumar abubuwa da dama da suka hada da: makullan babura da tsabar kudi da kusoshi da rezar feke fensuri da layin SIM da kuma mayen karfe.

Dokta A.R. Benkateswaran, ya ce sun sallami Jayakumar kuma yana cikin koshin lafiya.

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno

Lokacin Soke Tallafin Mai A Najeriya Ya Yi —Dangote

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta sha daƙile yunƙurin hargitsa ƙasar

Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m