Likitoci sun ciro karafuna masu nauyin giram biyar daga cikin majinyaci

A wani aikin tiyata da aka yi w awni majiyaci, likitocin Madhya Pradesh da ke gundumar Rewa a kasar Indiya, sun ciro sulalla 263 da tsinken karfen rezar gyaran fuska, wadanda kimar nauyinsu ya kai kilo biyar duk a cikin marasa lafiyar. Don haka likitocin suka ce an killace mutumin an aba shi cikakkiyar kulawa. […]

Likitoci sun ciro karafuna masu nauyin giram biyar daga cikin majinyaci

A wani aikin tiyata da aka yi w awni majiyaci, likitocin Madhya Pradesh da ke gundumar Rewa a kasar Indiya, sun ciro sulalla 263 da tsinken karfen rezar gyaran fuska, wadanda kimar nauyinsu ya kai kilo biyar duk a cikin marasa lafiyar. Don haka likitocin suka ce an killace mutumin an aba shi cikakkiyar kulawa.

Likitan ya ce an sha duba lafiyar Maksood a asibitin Satna tsawon wwata shida kafin a kawo Rewa.

Majiyacin mai shekara 32, mai suna Mohammed Maksood, ya fitto ne daga Sohabal a gundumar Satna, inda aka kai shi asibitin gwamnati na Sanjay da ke karkashin kwalejin horar da jami’an lafiya ta Gandhi Medical College ranar 18 ga Nuwambar bana, bayan da ya koka kan ciwon cikin da yake fama da shi.

Dokta Priyank Sharma na asibitin kwalejin horar da likitoci ta Sanjay Gandhi, ya bayyana wa kafar yada labarai ta PTI a Lahadin da ta gabata cewa sun gano dalilin da ya haifar wa Maksood ciwon ciki, bayan da suka dauki hoton cikinsa tare da wasu sauran gwaje-gwaje.

Ya ce rukunin likitocin da suka yi wa majiyacin tiyata sun fitar da tsinken karfen gyaran fuska 10 zuwa 12 da manyan allurai hudu da sarka da kwandalolin sulalla 263, baya ga balli-ballin gilasai, wadanda in an hada karikitan nauyinsu ya kai kilo biyar, wadanda duk daga cikin Maksood aka fitar da su ranar Juma’ar da ta gabata.

 “Majiyacin bai san inda kansa yake ba, kuma alamu sun nuna cewa ya hadidiyi wadannan karitai ne a asirce,” a cewar Dokta Sharma, inda ya kara da cewa Maksood a halin yanzu yana murmurewa a karkashin kulawar kwararrun jami’an kula da lafiya.

DAGA LARABA: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano