Likitoci sun ciro kwaron da ke rayuwa a cikin kunnen wata
Bayan wata mata mai kimanin shekara 50 ta dade tana fama da ciwo da kuma jin wani sauti a cikin kunnenta, sai ta ziyarci asibiti a kasar Thailand inda likitoci suka gano wani kwaro yana rayuwa a cikin kunnenta. Likitocin asibitin sun gudanar da bincike ne kan abin da yake cikin kunnen matar kuma an […]
Bayan wata mata mai kimanin shekara 50 ta dade tana fama da ciwo da kuma jin wani sauti a cikin kunnenta, sai ta ziyarci asibiti a kasar Thailand inda likitoci suka gano wani kwaro yana rayuwa a cikin kunnenta.
Likitocin asibitin sun gudanar da bincike ne kan abin da yake cikin kunnen matar kuma an yi sa’a sun gano kwaron da ke rayuwa a cikin kunnen, bayan da matar ta ce tana jin karar wani abu koyaushe a cikin kunnenta.
A lokacin da likitoci suka yi bincike sun razana da ganin yadda kwaron ya shige can cikin kunnenta yana yawo.
Likitocin sun yi amfani da na’ura wajen ciro kwaron daga cikin kunnen matar.
Matar ta ce, saboda azabar ciwon kunnen da take fama da shi a lokacin, tana da karnukan da sai sun gaji da haushi a cikin tsakiyar dare sannan su zo su kwanta a gadonta tana kallonsu, amma ba ta iya yin barci ko kadan.
Likitan da ya ciro wa matar kwaron mai suna Piradee Chanmonthon, ya ce matar ta auna arziki domin da kwaron ya yi kwayaye a cikin kunnenta da ya haddasa babbar matsala wajen cire su tare da kwaron, kuma ba za a iya cirewa cikin sauki ba har sai an yi tiyata a kunnen.