Likitoci sun ciro sarkokin zinare na Naira miliyan 24 a cikin maijinyaciya
Wata budurwa mai suna Runi Khatun, a Jihar West Bengal da ke kasar Indiya ta yi ta fama da ciwo inda hakan ya sa ta rika amai, daga nan aka yi gaggawar kai ta asibiti. Bayan an kai Runi, mai kimanin shekara 26 asibiti, likitoci sun yi mata tiyata inda suka ciro karafuna da wasu […]
Wata budurwa mai suna Runi Khatun, a Jihar West Bengal da ke kasar Indiya ta yi ta fama da ciwo inda hakan ya sa ta rika amai, daga nan aka yi gaggawar kai ta asibiti.
Bayan an kai Runi, mai kimanin shekara 26 asibiti, likitoci sun yi mata tiyata inda suka ciro karafuna da wasu sarkokin zinare da aka kiyasta kudinsu zai kai kimanin Naira miliyan 23 da dubu 850.
Likitocin asibitin West Bengal a Indiya, sun gano cewa, budurwar tana dauke da wani gurbi a cikinta da yake dauke wadannan karafunan da suka hada da: sarkoki 69 da ’yan kunne 80 da kudaden karfe 46 da sarka mai kwado 8 da zoben da ake sawa a hanci 11 da sarkar da ake sawa a kafa 5 sai kuma wani karfen agogo 1.
A cewar mahaifiyar Runi, an rika samun bacewar sarkokin zinare a gidan, amma duk da haka ba ni da masaniya kan yadda Runi ta rika hadiyar tarin sarkokin.
Mahaifiyar Runi ta kara da cewa da alamu mafi yawan sarkokin an same su ne daga shagunan dan uwanta.
A duk lokacin da aka tuntubi Runi game da bacewar wata sarka sai ta fara kuka, amma ta ki bayyana cewa ita ce ke hadiye sarkokin.
Duk ’yan uwan Runi, sun ce a kowane lokaci idan aka samu bacewar sarkokin gidan sai a tambayi Runi, amma ba za ta amsa cewa ita ke hadiyewa ba, sai kawai ta fara kuka.
Mahaifiyar Runi ta kara da cewa, Runi ba ta da lafiya kimanin wata biyu ke nan, sanadiyyar hadiyar sarkokin da take yi.
Kafin a kai Runi asibiti gwamnati na Rampurhat, an fara kai ta wasu asibitoci masu zaman kansu, inda aka yi ta magani amma babu wani sakamakon binciken rashin lafiyar.
Likitocin sun ce, mafi yawan karfunan tagulla ne da brass.
Shugaban tiyatar Dokta Siddhartha Biswas, na asibitin Kwalejin Gwamnati Rampurhat, ya ce Runi, ba za ta iya cin abinci ba saboda ciwon ya yi tsanani.
Dokta Siddhartha, ya ce jikin Runi ya yi tsanani lokacin da aka kawo ta asibitin, don haka suka jinkirta yi mata tiyatar gaggawa.
A yanzu haka Runi, na bukatar karin jini da ya kai akalla leda biyar.