Likitoci sun ciro tarin gashi daga mahaifar wata

Bayan yawan fama da ciwon ciki da wata mata uwar ’ya’ya biyu, ke yawan kuka a kai, likitoci sun yi nasarar ciro tarin gashi a cikin mahaifarta bayan sun yi mata tiyata. Likitan da ya yi wa matar tiyata ya ce, an samu nasarar yin tiyata ga matar mai shekara 30, kuma ta haifi ’ya’ya […]

Likitoci sun ciro tarin gashi daga mahaifar wata

Bayan yawan fama da ciwon ciki da wata mata uwar ’ya’ya biyu, ke yawan kuka a kai, likitoci sun yi nasarar ciro tarin gashi a cikin mahaifarta bayan sun yi mata tiyata.

Likitan da ya yi wa matar tiyata ya ce, an samu nasarar yin tiyata ga matar mai shekara 30, kuma ta haifi ’ya’ya biyu. Tsawon tarin gashin da aka ciro ya kai inci biyar yana cikin mahaifar tun lokacin da aka haife ta.

Matar da aka sakaya sunanta ’yar kasar Rasha ce da ta yi ta fama da ciwon ciki kafin a yi mata tiyata.

Babbar Likitar Cibiyar Kula da Lafiya Mata Masu Juna Biyu ta Kolomna Perinatal Centre, Dokta Tatiana Shabrak, ta ce: “Tarin gashin ya maye wani gurbin wata halitta ce da ke cikin mahaifarta.”

Tarin gashin yana hade ne da wata tsoka manne da fata da kitse da kashi sannan an samu hakori a ciki.

A cikin gurbin da aka samu tarin gashin, an samu nasarar gano su ne ta hanyar amfani da na’urar daukar hoton cikin mutum, kuma ba a samu wata tangarda ba wajen yin tiyatar.

Akwai kusan bangarori hudu a cikin tarin gashin da ya yi tsawo a cikin mahaifar.

Ma’aikatar Lafiya ta birnin Moskow ce ta fitar da hotunan tiyatar.

Likitar asibitin ta ce wannan tarin gashin da aka samu wata irin halitta ce da za a iya  gadonta.

”Matar tana dauke da wannan halittar ce tun tana yarinya, amma ba wanda ya iya sanin halittar na ci gaba da girma.

Hakan zai iya faruwa a tsakanin shekara 15 zuwa 30 har zuwa 70. Wannan gurbin da aka samu gashin yana iya girma a cikin mahaifar,” inji ta.