Likitoci sun fara yajin aiki a Jihar Edo
Qungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jihar Edo ta fara yajin aiki na wuni biyar don gargaxi ga hukumomin jihar, sakamakon tavarvarewar yanayin kula da haqqoqinsu da qarancin ma’aikatan lafiya a asibitocin jihar da sauran dalilai makamantansu. A yayin da yake ganawa da ’yan jarida kan batun, jim kaxan daga fitowarsu daga taron gaggawa, Shugaban Qungiyar […]

Qungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jihar Edo ta fara yajin aiki na wuni biyar don gargaxi ga hukumomin jihar, sakamakon tavarvarewar yanayin kula da haqqoqinsu da qarancin ma’aikatan lafiya a asibitocin jihar da sauran dalilai makamantansu.
A yayin da yake ganawa da ’yan jarida kan batun, jim kaxan daga fitowarsu daga taron gaggawa, Shugaban Qungiyar Likitoci ta Jihar Edo, Dokta Emmanuel Osaigbovo ya ce duk wani likita a jihar, a qarqashin jiha ko tarayya, yana cikin wannan yajin aiki da nufin sama wa ’ya’yan qungiyarsu haqqoqinsu.
“Sama da shekara xaya muke ta yi wa gwamnatin Jihar Edo qorafi cewa ana yi mana wariya game da jin daxin aikinmu. Mun ba da wa’adi da dama cewa a kula da haqqoqinmu amma muka saurari uzuri, ganin cewa wasu muhimman mutane suna ba mu haquri, amma yanzu dole ce ta sanya muka tsunduma cikin yajin aikin na gargaxi,” inji shi.
Ya ce akasrin asibitoci da cibiyoyin lafiya na jihar sun lalace kuma gaba xaya jihar tana da likitoci 200 ne. Ya ce a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta ba Ma’aikjatar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya kyautar na’urorin xaukar hoton majinyata, alhali ita ba ta da ko xaya a asibitocinta.
A nasa vangaren, a lokacin da yake bayyana matsayar Gwamnatin Jihar Edo, Kwamishinan Lafiya, Dokta David Osifo ya nuna rashin jin daxinsa kan yajin aikin, ya ce Qungiyar Likitoci tana sane da duk irin qoqarin da jihar ke kan yi wajen magance matsalolin kiwon lafiya a jihar, kasancewar tana xaya daga cikin kwamitocin da ke bin kadin shawo kan matsalolin lafiya a jihar.
“Gwamna ya kafa kwamiti domin tantance matsalolinsu da kuma abin da suke buqata kuma muna aiki tare da su likitocin,” inji shi.