Likitoci sun fara yakin aiki kan garkuwa da abokiyar aikinsu

Wata takwas bayan sace Dokta Ganiyat, har yanzu ita da ɗan ɗan uwan mijin nata suna tsare a hannun ’yan bindigar

Likitoci sun fara yakin aiki kan garkuwa da abokiyar aikinsu

Likitoci

Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa (NARD) ta fara yajin aikin gargaɗi a faɗin Najeriya, don nuna bacin ransu kan garkuwa da aka yi da abokiyar aikinsu, Dokta Ganiyat Popoola-Olawale, domin karɓar kuɗin fansa.

Ƙungiyar ta ce ta yanke shawarar fara yajin aikin ne a taton gaggawa na majalisar zartarwarta na ranar Lahadi.

“Majalisar Zartarwa ta NARD ta yi ittifakin fara yajin aikin gargaɗi na mako guda daga karfe 12 na dare kafin wayewar garin Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024,” a cewar sanarwar bayan taron.

Sanarwar ma ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar NARD, Dokta Dele Abdullahi Olaitan, da Sakataren kungiyar, Dokta Anaduaka Christopher Obinna da Sakataren kula da jin dadi, Egbe John Jonah, ta ce, “Abin baƙin ciki ne yadda aka ci gaba yin garkuwa da abokiyar aikinmu, Dokta Ganiyat Poopola, duk kuwa da ƙoƙarin gwamnati da jami’an tsaro na kuɓutar da ita.”

Ana iya tuna cewa a kwanakin baya kungiyar ta ba da wa’adin mako biyu a sako Dokta Ganiyat, in ba haka ba, mambobinta su ɗauki matakin da ya dace.

A ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2023 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da likitar a gidanta da ke rukunin gidajen ma’aikatan Asibitin Ido na Ƙasa da ke Kaduna.

An yi garkuwa da ita ne tare da mijinta da wani ɗan ɗan uwansa da ke zaune da su a gidan.

Bayan watanni uku ana tattaunawa da su, a ranar 7 ga watan Maris, 2024 ’yan ta’addan suka sako mijin likitar, Nuruddeen Poopola.

Sai dai har yanzu, wata takwas bayan sace Dokta Ganiyat, har yanzu ita da ɗan ɗan uwan mijin nata suna tsare a hannun ’yan bindigar.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana