Likitoci sun gano kwaron da ke shan jini a hancin wani mutum

Likitoci a birnin Dien Bien Phu, a kasar Bietnam sun gano wani kwaro mai ban al’ajabi da ke rayuwa a hancin wani mutum da aka sakaya sunansa, kwaron dai na shan jinin mutumin ne. Likitocin sun gano kwaron ne lokacin da mutumin ya kai kansa asibiti hancinsa na zubar da jini da yi masa ciwo. […]

Likitoci sun gano kwaron da ke shan jini a hancin wani mutum

Likitoci a birnin Dien Bien Phu, a kasar Bietnam sun gano wani kwaro mai ban al’ajabi da ke rayuwa a hancin wani mutum da aka sakaya sunansa, kwaron dai na shan jinin mutumin ne.

Likitocin sun gano kwaron ne lokacin da mutumin ya kai kansa asibiti hancinsa na zubar da jini da yi masa ciwo. Likitocin sun razana lokacin da suka binciko kwaron da ke rayuwa a hancin dan Adam. Sun yi amfani da kyamara wajen tantance irin wannan halitta da ke rayuwa a hancin dan’ Adam, wannan kwaron dai an gano shi a cikin ramin hancin mutumin.

Dokta Tuan ne ya gano kwaron kuma ya ciro shi daga cikin hancin ta hanyar amfani da kyamara wajen gano gurbin da kwaron yake.

A cewar rahoton mara lafiyar da aka sakaya sunansa wand mazaunin wata unguwa ce da ke birnin ya ziyarci asibiti ne lokacin da yake fama da ciwon fuska da kuma zubar jini a hancinsa. Bayan da likitan ya yi nasarar cire kwaron daga cikin hancinsa, sai ya shawarce shi da ya dai na shan ruwa daga korama saboda akwai yiwuwar samun kwaron da zai iya haifar da irin wannan cutar ta hanyar shan ruwa.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana