Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu
Ƙungiyar likitocin tana umartar ɗaukacin mambobinta da su koma aiki a yau Lahadi.
Likitoci a bakin aiki
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal.
Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki.
- Mun kori Falasɗinawa sama da dubu 250 daga Gaza — Isra’ila
- Trump ya buƙaci ƙasashen NATO su daina cinikin man fetur da Rasha
Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi.
Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su.
Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da walwalar ma’aikata.
A ranar Alhamis ce ƙungiyar likitocin ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema.
Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba.
Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko.
Tun dai cikin wata sanarwa da ƙungiyar likitocin ta fitar a ranar 1 ga Satumba, 2025, ta buƙaci a biya mambobinta bashin ƙarin albashin watanni biyar da suka biyo, bayan aiwatar da ƙarin albashi tsakanin kashi 25 zuwa 35 cikin 100 da aka amince wa ma’aikatan lafiya.
Haka kuma, likitocin sun gabatar da wasu buƙatun da suka haɗa da gaggauta biyan su bashin alawus-alawus ɗinsu da kuma sauran buƙatu da suka shafi jin daɗin aiki da walwala.
Likitoci masu neman ƙwarewar aiki a Najeriya su ne ƙashin bayan aikin kiwon lafiya a ƙasar, inda suke gudanar da ayyuka asibitoci mallakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.
Duk lokacin da suka shiga yajin aiki ana samun koma baya wajen kiwon lafiyar al’umma, lamarin da ke jefa rayuwar marasa lafiya ciki halin rashin tabbas.