Likitoci sun janye zanga-zangar da suka shirya

Likitoci Masu Neman Kwarewa sun janye zanga-zanar gama-garin da ta shirya farawa a fadin Najeriya a yau Laraba.

Likitoci sun janye zanga-zangar da suka shirya

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa (NARD) ta janye zanga-zanar gama-garin da ta shirya shiga a fadin Najeriya a yau Laraba.

Shugaban kungiyar, Dokta Orji Emeka Innocent, ya ce majalisar kolin kungiyar ta yanke shawarar ne bayan taron da ta yi ranar Laraba da dare.

Sai dai ya ce cikin sa’o’i 72 masu zuwa kungiyar za ta sake zama ta kara nazari kan matakin janye zanga-zanar.

Da farko NARD ta shirya gudanar da zanga-zanga a kullum ta hanyar rufe cibiyoyin lafiya mallakin gwamantin tarayya daga karfe 10 na ranar Laraba 9 ga watan Agustan nan da muke ciki.

Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi

Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai

Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa