Likitoci sun tsunduma yajin aiki a ABUTH

Likitocin sun fara yajin aikin gargaɗin ne a ranar Litinin.

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a ABUTH

Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD), a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar.

Sun fara yajin aiki ne saboda rashin biyan wasu daga cikin mambobinsu albashinsu.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Dokta Ashiru Mikail, ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Zariya.

Ƙungiyar ta bai wa hukumar asibitin wa’adin mako guda don biyan buƙatunsu nan da ranar 15 ga watan Yuli, amma suka gaza cimma matsaya.

Dakta Mikail ya bayyana cewa ƙungiyar ta ƙi amincewa da biyan mambobinta da ke amfani da dandalin GIFMIS wani kaso na albashin.

A watan Yuni, an rage albashin likitocin da abin ya shafa da kusan kashi 25 zuwa 27, wanda ya kai N58,000 zuwa N60,000.

Bugu da ƙari, waɗannan likitocin suna bin bashin albashi tun daga 2021.

Duk da yanayin tattalin arziƙi da matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan, hukumar kula da asibitocin ba ta ce uffan kan rage albashin ba.

Hukumar gudanarwar ta ba da shawarar biyan Naira miliyan biyu a duk wata daga kuɗaɗen da ake kashewa don biyan bashin da suke bi.

Hakan na nufin kowane mamba zai samu Naira 5,000 ne a kowane wata, maimakon Naira 100,000 da kowa ke karba a baya.

Sama da kashi 60 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya na tarayya da ke Arewa maso Yamma sun fara biyan wadannan basussukan.

Sai dai ABUTH ya bayar da shawarar biyan Naira 5,000 kawai maimakon Naira 25,000.

Yanzu haka dai likitocin sun shiga yajin aikin don gargaɗin hukumomin gudanarwar asibitin ABUTH.