Likitoci sun yi barazanar fara yajin aiki a Jihar Kano

kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Kano ta nemi gwamnatin jihar ta biya ’ya’yanta hakkokinsu, don kauce wa shiga yajin aiki.Sabon Mataimakin Shugaban kungiyar ta Jihar Kano, Dokta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyana haka a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda ya ce kungiyar ta ba gwamnatin Jihar Kano wa’adin makonni biyu […]

Likitoci sun yi barazanar fara yajin aiki a Jihar Kano
Likitoci sun yi barazanar fara yajin aiki a Jihar Kano

kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Kano ta nemi gwamnatin jihar ta biya ’ya’yanta hakkokinsu, don kauce wa shiga yajin aiki.
Sabon Mataimakin Shugaban kungiyar ta Jihar Kano, Dokta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyana haka a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda ya ce kungiyar ta ba gwamnatin Jihar Kano wa’adin makonni biyu ta biya wadannan hakkoki ko su shiga yaji.
Mataimakin Shugaban ya kara da cewa a yanzu haka ana tattaunawa da gwamnatin don nemo bakin zaren, inda kuma ya nemi masu ruwa da tsaki a harkar kula da lafiya da ke jihar su ba gwamnati shawara game da illar da yajin aikin zai iya haifarwa ga al’ummar jihar.
Dokta Sanusi ya ce likitoci a jihar za su gudanar da wani shiri na duba marasa lafiya kyauta a cibiyoyin gyaran hali na Mariri da Tudun Maliki. “Kamar yadda muka saba za mu gudanar da duba marasa lafiya kyauta a jihar nan a Tudun Maliki da Mariri.  Bayan mun duba su za mu ba su magunguna tare da taimaka musu da shawarwari a kan kula da lafiyarsu,” inji shi.